Wasiyyar Masanin Binciken Noma Ana Saura Kwana 5 Ya Rasu!

Manoman Alkama

Ci gaba daga makon jiya…

A makon da ya wuce, mun tsaya da tattaunawar ta mu ne, inda marigayin ya nuna yadda marigayin ya kai ISra’aila, inda ya ga yadda suke aikin zuma, wanda ya sa har ya yi kokarin kawo wannan fasaha wadda kuma a halin yanzu ake da shahararren masanin harkar kiwon zuma a kasar nan. Ga ci gaban hirar..

Idan muka dawo wannan kasa batun gwamnati da take yi na kokarin bunkasa harkar noma, wanda ake ganin kamar yana daya daga cikin jiga-jigai na tattalin arziki, yanzu ma akwai shiri na cewa za a bunkasa harkar noma, ya kake ganin wannan abu zai yi tasiri?

Ai tuntuni, mu in na tambaye ka, ko ka san Garba ABCD? To tun daga shekara ta1980 zuwa 1970, ni ne mai ba su tsare-tsare, suna gabatar da wasu “programmes” ni ne “producer” na shirin, zan kira su mu yi hira da su ga abin da za su yi,sai su rike wani lokaci a rubuta amsoshi da manoma suka bayar, sai su zauna su tattauna, to tun a lokacin nake cewa, in fa ba a mai da hankali a aikin noma da kiwo ba, nan gaba a kasar nan za a yi ladama.

wannan fetur ana hako shi ne, yana karewa, akwai lokacin da za a zo farashin fetur za ta fadi kasa warwas, ko an hako shi ma ba riba, saboda haka, a mayar da hankali ga noma, mu abin da muka fahimta game da noma musamman a arewa, wato yanayinmu, yanayi ne mai ban mamaki, abin da ake cewa, ba a yinsa sai a “Mediterranean climate” wallahi ana yinsa a nan, su apple din nan, duk irin wadannan ‘ya’yan itatuea da za ka ga ana kawowa daga can, duk ana yinsu a nan suna yi, da waken suya ba a noma shin a ko’ina sai a Benue, muka ce a’a ai yana yi a ko’ina, aka gwada a Sakkwato yana yi da Kano. yanzu waken suya ko’ina yana yi ka gani ko?

Ridi shi ma haka ne, rake wannan da ka sani, wannan mai jan jiki din nan katon nan ai da ba shi ne ba, rakenmu wani dan siriri ne,wajen Makarfi ake noma shi. Sai wata shekara ciwon amful ya kama shi, wanda za ka ga raken ya yi ja, kuma in ka sha za ka ji ya yi tsami,daga nan ne aka kawo wani iri wannan ake ce masa “Kantoma” ina ganin daga wajen Brazil ne aka kawo shi, abubuwa da yawa da aka shigo da su,an ce ba sa yi sai a Europe, ina! Ga su nan ana yi ko ina a cikin gidanka ma in kana so sai ka noma shi,ko ina a kasar nan,muna da yanayi mai kyau.

Saboda haka, in ba a koma noman ba za a ga ashe an yi kamun gafiyar baidu ne

Wannan ya fito a guje ka jefi wannan da na hannunka, duk sun gudu, sannan kiwo shi ma mun yi ta magana akai.

Na ga yadda ake yin kiwo irin na zamani, makiwaci daya sai ka ga yana da shanu dubu ko dubu biyu, abincinsu a nan ake nomawa,ba sai an fitar da su kiwo ba, maciji ya sare su, kudan tsandu ya cije su.

Mun sha magana a kan wannan cewa, nan gaba fa dole a komo a yi wani abu. To shi ne wasu jihohi ke kokarin su yi wannan tsari,

wanda suke kira da Ruga. Ba kiwo irin na ruga ba ne, sunan ne dai kawai.

Wato kiwo ne na gaske za ka ga ana wa shanu baye, da shanun waje masu ba da nama ko nono mai yawa.

Sannan a bangaren kiwon zuma, na ga wasu abubuwan ma da ake yi da kakin zuma da wasu abubuwan ma da mutanenmu ke batawa, ka san mutanenmu in za a sha zuma a kan je da wuta ne a kokkona kudan zuma. Subhanallahi! Ba haka ake yi ba, akwai yadda ake yi.

Da na ga irin wannan abu, naga amfanin zuma sai na ce, don Allah su turo mana wasu mana, sai suka turo mutum biyu, sai na zo na samu gwamnatin lokacin muna karkashin Ma’aikatar kimiyya da fasaha shi ke nan suka yarda za su ba mu kudi a yi “training” su kuma wadannan mutane “staff” dinsu sannan aka gayyaci kowa duk daga Nijeriya har daga kasashen waje daga Afirka ta yamma, akai mako uku ana “training” a kan yadda ake kiwon zuma.

Akwai yarona wan wannan Abubakar to shi ne yaronmu na farko, ana ce masa Idris, to shi ma “Agricultural Edtension Worker” ne ya zo ya yi “training” din nan, yanzu in gaya maka shi din nan kusan shi ne “best” mai aikin zuma a Afirka ta yamma. Ya je China ya yi watanni, ya tafi Sierra Leone, ya tafi Italy,yanzu shi “consultant” ne ya yi ritira aikin zuma kawai yake yi.

in ka ga yadda yake rike zuma sai ka gudu.

Yadda na ga zumar nan a Isra’ila, abin mamaki ne, suna tace zuma za ka ga mutum da akwati kusan dari biyu a bayan gida kuma yana da lambun itatuwan lemu a nan suke shan huda, kuma abin da yake yi, da akwatunan nan bayan suna ba shi zuma da sauran abubuwa “product” na zumar yana ba da hayar zuman ga manoma idan ya ba da haya, su ne za su je su ruka “pollinating” ka ga, ya samu riba biyu.

Bayan wannan sai kuma kiwon kifi da sauran abubuwa, wato kiwon kifi a can na ga wani abu mai ban mamaki, tarwada din nan ka gansu da zane-zane kamar wani “artist” ne ya ya yi zanen.

Ya kake Ganin Yadda Za Magance Matsalar Sare Itatuwa?

Maganin kwaya daya ita ce, a koma yadda yakamata a samu gurare-gurare a dasa itatuwa, za a dasa su ne, matakai-matakai, kowace shekara mai zuwa idan aka yanke wannan wancan kuma zai taso, ana yanke wani, wani kuma na tasowa, haka za a yi ta yi, kuma ba wai za a samu wani guri kawai ba a ko’ina za a yi, yanzu misali akwai maganar itace ko kuma katako,wanda ake sare itace ake yi, ba a dasa itace na musammam a tsare wanda za a yi katako da shi. Da ana yin haka da ba a samu matsala ba

Kana da wani sako da kake so ka isar ga al’umma?

Sakona na karshe, ga al’umma shi ne mu hada kai, mu daina zagin shugabanni, mu taimaki junanmu, mu dage wajen neman ilimi da yin aiki da shi, mu taimaki al’umma

Ranka ya dade godiya muke.

To Alhamdulillahi.

Exit mobile version