Majalisar wakilai ta yi kira ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari (retd.), Da ya ba da umarnin a sake bude wani bangare na makarantu don ba dalibai damar su zauna a Makaranta don rubuta jarrabawar WAEC ta shekara 2020.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a zaman da ta gabatar ranar Talata bayan amincewar da wani dan majalisa, Nnolim Nnaji ya yi.
Kwamitin ilimi da aiyuka ya bayyana a ranar juma’ar da ta gabata inda ta yi fatali da shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yi na dakatar da shirin sake bude makarantu don daliban aji na karshe su zaina suyi arrabawar.
Kwamitin ya yi Allah-wadai da shawarar da ta hana daliban Najeriya zama don rubuta jarrabawar WASSCE da za a gudanar na shekarar 2019/2020.