Daga Abubakar Abba, Kaduna
Ministan kasuwanci da Masana’antu da Zuba Jari Okechukwu Enelamah da takwaran sa Ministan Harkokin Kasashen waje Geoffrey Onyeama sun baiwa ma su son zuba jari dake kasar Amurka tabbacin cewar Gwamnatin Najeriya zata samar ma su da yanayi mai inganci don su zo su zuba jarin su a kasar, da kuma yi ma su alkawarin dinbin ribar da ba a taba samu ba a duk fadin duniyar nan.
Sun bayar da tabbacin ne a taron ma su ruwa da tsaki tsakanin Najeriya da Kasar Amurka akan harkar kasuwanci da zuba jari da aka gudanar a kasar Amurka.
Enelamah ya ce, gwamnatin tarayya tana da burin gina sabuwar Najeriya, inda zata sha ban-ban da a yadda take a baya.
Onyeama ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya baza ta baiwa ma su son zuba jari daga kasar Amurka kunya ba, musamman ganin tuni, wasunsu sun fara zuba jarin su kasar nan ta hanyar wanan kungiyar.
Ya ce, zamu yi ma su rigista da basu dama ta hanyar shige da fuce da dukkan nin abubuwan da suka dace na shigowa kasar don zuba jarin su.
Ministan ya ce, zamu samar ma su da babbar hada-hadar kasuwanci dake da kimanin jama’a miliyoyi dare tsasa’in da uku. Ya ce “ zamu kuma tabbatar masu da shugabanci na gari da samar ma su tsaro”.
Ministan ya ce, “zamu yi dikkan abin da ya dace wajen mai da kasar nan wata sabuwar duniya.”
Onyeama ya ce, “zamu maida ofis-ofis din mu na jakadanci dake kasashen waje har da kasar Amurka zuwa waja jen kasuwanci da kuma samar maku da duk kan bayanai da kuke so akan Najeriya don ku samu sukunin zuba jari.
Babbar Sakatariya ta Hukumar zuba jari da habaka kasuwanci Yewande Sadiku, ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta sa ran za a zuba jari har na Dalar Amurka Biliyan 25 a shekarar 2020.
Sadiku ta ce, gwamnatin tarayya tana sane da matsalar masu son zuba jari a kasar suke fuskanta, inda tasha alwashin cewar, za a magance matsalar.
Shima a nashi jawabin a wurin taron, Manajin Daraktan Ma’aikatar zuba jari Anthony Orji,yace a shekara daya data wuce, maaikatar ta samu cin nasara wajen yin hadin gwiwa don habaka aikin noma.
Ya bayyana cewa,” mun zuba Dalar Amurka miliyan 25 a harkar habaka noma a Kasar Afirka ta Kudu,inda a yanzu aka samar da Dalar Amurka 150.