CRI Hausa" />

Wasu Ba Su Da Dalili Da Da’a, Sun Yunkura Kasar Sin Ta Biya Musu Diyya

Kwanan baya, wasu kafofin yada labarun kasar Birtaniya sun ce, tawagar nazari ta Henry Jackson Society mai hedkwata a birnin London, ta kaddamar da rahoton nazarinta, inda a cewarta, kasar Sin ta boye bayanan yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, wanda hakan ya sabawa ka’idojin kiwon lafiya na kasa da kasa. Don haka wajibi ne kasar Sin ta sauke nauyin yaduwar annobar a duniya. Tawagar ta kuma yi shelar cewa, ya kamata kasashen duniya su bi bahasin lamarin, don neman samun diyya daga kasar Sin.

Ko shakka babu, alaman wannan tawaga ba su da ma’ana ko kadan. Sanin kowa ne cewa ta hanyar babbar sadaukarwa, Sin ta gina shinge mai karfi na dakile yaduwar annobar, tare da tanadar lokaci mai tsada na shawo kan cutar. Ta sanar da bayanan yaduwar annobar, ta kuma yi mu’amala da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da kasashen duniya, dangane da dabarun kandagarki da dakile yaduwar annobar, da kuma ba da magani ga masu kamuwa da cutar ba tare da rufa-rufa ba. Kasashen duniya da dama ma sun amince, da kuma jinjina abubuwan da kasar Sin ta yi.
Kalaman neman kasar Sin ta biya diyya, ba su da dalili, kuma babu da’a a cikin su.
Birtaniya tana da ingatattun fasahohin kiwon lafiya, amma matsalar karancin albarkatun kiwon lafiya, da kuma gazawa wajen mai da hankali kan bayanan da kasar Sin ta gabatar, su ne suka haifarwa Birtaniya cikas, wajen daidaita irin wannan matsala ta kiwon lafiya ta ba-zata yadda ya kamata.
Masana masu tsattsauran ra’ayi, da ’yan siyasan jam’iyyar Conservative, wadanda suka goyi bayan manufofi na kuskure, su ne wadanda ya wajaba su yi tunani sosai kan abubuwan da suka aikata.
Yanzu haka, yawan wadanda suka kamu da annobar ya wuce miliyan 1 da dubu 200 a duk fadin duniya. Yayin da ake kokarin yaki da ita a duniya, wasu kungiyoyi da ’yan siyasa na kasashen Turai da Amurka, sun yi aikace-aikace bisa ra’ayin wariyar launin fata, sun kuma dora wa kasar Sin laifin hakan, sun kuma kara kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar.
Yayin da annobar take yaduwa a kasashen Turai da Amurka, wadannan marasa da’a, su ne ya wajaba a gurfanar a gaban kotu, domin sun yi fatan ganin kura ba ta kwanta ba a duniya, a yunkura cimma mumunan burinsu. (Masu Fassarawa: Tasallah Yuan)

Exit mobile version