Connect with us

LABARAI

Wasu Daga Cikin Shugabannin Manyan Makarantu Ba Su Da Hali Mai Kyau – Minista

Published

on

Ministan ilimi, Adamu Adamu ya ce, wasu daga cikin shugabannin manyan makarantun kasar nan sam ba su da sanin ya kamata wajen gudanar da ayyukan da ya hau kansu.

Ministan ya fadi hakan ne wajen taron tattauna tsarin jarabawar ta JAMB ta wannan shekarar 2018, tare da dukkanin manyan makarantun kasar nan, wanda aka yi a babban zauren taro na, Bola Babalakin, da ke Gbongan, ta Jihar Osun.

Ya bayyana cewa, yawancin halayen da yawan shugabannin Jami’o’i, da shugabannin kwalejojin kimiyya da fasaha da na manyan jami’ansu, “Sam kare ma ba zai ci ba.”

“Wasu daga cikinku, suna gudanar da ayyukansu ne tare da sanin wasu halayen naku ba masu kyau ne ba.

“Muna nan mun taskace tabbataccen bayanan wasu daga cikin halayen banzan naku da kuma abubuwan da ku ka yi wadanda sam ba su dace ba, da suka hada da, daukan dalibai ba bisa ka’ida ba, cinye kudade da kuma rashin bin dokoki kamar yadda aka tsara.”

Ministan ya ce, keta haddin dokokin da aka shimfida, abu ne da ba za a lamunta ba, duk kuma wata cibiyar da aka samu da laifin aikta hakan tabbas za a hukunta ta.

Ya yi gargadin kar wata makaranta ta sayar da takardar neman shiga cikinta a sama da Naira 2000.

Shi ma da yake magana a wajen, magatakardan hukumar ta JAMB, Ishak Oloyede, cewa ya yi, a yanzun ana samun daidaito da duba jarabawar ta JAMB yadda ya kamata, domin ana farawa da kuma karewa ne a tare.

 
Advertisement

labarai