Abba Ibrahim Wada" />

Wasu Daga Cikin ’Yan Wasan Liverpool Sun Warke

'Yan Wasan Liverpool

kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sanar da murmurewar wasu daga cikin ‘yan wasanta da ke jinya, wanda ya haddasa mata gagarumar koma baya a wasanninta na Firimiya cikin wannan kakar wasan.

Cikin ‘yan wasan Liverpool da aka ga kafarsu a filin atisaye a ranar Litinin bayan jinyar sun hada da dan wasan kasar Mali Naby Keita wanda rabon da ya bugawa Liverpool wasa tun nasarar tawagar akan kungiyar Crystal Palace da kwallaye 7 da nema cikin watan Disamba, sai kuma Dibok Origi da Ben Dabies wadanda rauni ya hanasu damar buga wasa a wasannin karshen mako da Liverpool din ta yi rashin nasara a hannun kungiyar kwallon kafa ta Leceister City da kwallaye 3 da 1.
Sai da har yanzu Liverpool ba ta sanar da warwarewar dan wasan tsakiya Fabinho na Brazil ba, ko da ya ke su kansu ‘yan wasan 3 da suka murmure babu tabbacin ko za su iya buga wasa musamman a karawar  gasar cin kofin zakarun Turai.
Tawagar Jurgen Klopp wadda ta rasa damar shiga Jamus don karawa da RB Leipzig a zagayen farko na kungiyoyi 16 karkahsin gasar zakarun Turai, matakin da ya tilasta kungiyoyin 2 zabar kasar Hungary domin buga wasan da suka fafata a jiya Talata.
Liverpool Abin Tsoro Ne
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig Julian Nagelsmann ya ce daman ya na cike da fargabar haduwar tawagarsa da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai.
A kalamansa ya yin taron manema labarai gabanin karawar Liverpool da RB Leipzig a birnin Budapest, Nagelsmann ya ce rashin abin kirkin da Liverpool ke yi a wasannin Firimiya na baya-bayan nan ba shi zai basu kwarin gwiwar iya doketa a karawar ba.
Liverpool tayi tattaki zuwa birnin Budapest biyo bayan rashin nasara a wasanni 9 na Firimiya ciki har da rashin nasara 3 a jere wanda hakan yasa kungiyar yanzu ta fita daga cikin sahun kungiyoyin da zasu iya lashe gasar cin kofin firimiyar Ingila.
Ko a Asabar din da ta gabata Jurgen Klopp ya amsa cewa ba shi da tabbacin Liverpool za ta iya kare kambunta na Firimiya bayan rashin nasara a hannun Leicester City wanda ya kara tazarar da ke tsakaninta da Manchester City jagora zuwa maki 13.
A bangare guda kuma RB Leipzig na matsayin ta 2 ne a teburin Bundesliga kasa da Bayern Munich mai rike da kambun na zakarun Turai kuma mai koyar da tawagar ta RB Leipzig,  Nagelsmann ya ce sun yiwa karawar dukkan shirin da ya kamata.

Exit mobile version