Mahdi M Muhammad">

Wasu Dattawan Arewa Sun Nemi Buhari Ya Sauya Tsarin Tsaron Nijeriya

Wasu dattawa daga yankin arewa maso gabashin kasar nan, a jiya sun bayyana cewa, sun matukar damuwa da yadda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar, suna masu cewa uzurin da shugabannin rundunonin ke gabatarwa na rashin gudanar da aikin tsaron, ba abin dogaro bane yanzu.

A wata sanarwa da suka fitar a Abuja dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Mista Zana Goni, a karkashin kungiyar dattawan arewa maso gabas don Zaman Lafiya da ci gaba (CNEEPD), sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta aiwatar da kudurin da majalisar dokoki ta kasa ta zartar kwanan nan, suna kuma rokon shugaban kasa da ya sake duba tsarin tsaron kasar.

Sun yi nadamar cewa mutane sun yi kuskuren fahimta game da shirun nasu, tare da bayyana cewa yanayin shugabannin hafsoshin tsaron ba shi da wata alaka da hakan.

Advertisements

A cewarsu, yardar da suke da shi na cewa abubuwa za su gyaru kamar yadda shugabannin tsaro suka saba fada da kuma ba da tabbaci na shugaban kasa, hakan ya sa suka yi hakuri a farko.

 

Exit mobile version