Maigari Abdulrahman" />

Wasu Gwamnoni Sun Fara Nadin Mukamai Bayan rantsar Dasu

Wasu daga cikin sababbin gwamnoni sun fara nada sakatarorin gwamnati, a bangaren gwamnatin tarayya kuwa bata fara nada kowa ba.

Daga cikin jihohin da aka nada sakatarorin akwai jihar Adamawa, Bauchi, Legas, Yobe, Kano, da Akwa’ibom.

A jihar Adamawa, Injiniya Bashir Ahmad ne gwamnan jihar Fintiri ya nada a matsayin sakataren gwamnatin jihar, ya hore shi da ya gudanar da aikinsa ba tare da tsoro ko yin alfarma ba. Haka kuma, gwamnan ya nada babban dan jaridar nan, Solomon Kumangar a matsayin daraktan sadarwa da labarai na gidan gwamnati. George Kushi, wanda yake ma’aikacin gidan TB na AIT ne gwamnan ya nada a matsayin daraktan labarai.

A Bauchi, gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya nada Muhammad Sabi’u Baba a matsayin sakataren gwamnati, sai kuma Abubakar Kari a matsayin shugaban ma’aikata, sai Bashir Ya’u   mataimakin shugaban ma’aikata kamar yanda kakakin gwamnan, Ladan Salihu ya fitar a cikin wata sanarwa.

A jihar Legas, gwamna Sanwo-Olu ya nada tsohon shugaban ma’aikata a matsayin sakataren gwamnati. Sai kuma dan jarida Gboyega Akoshile a matsayin mataimakin sakataren labarai.

A jihar Yobe kuwa, gwamna Mai Bala Buni ya sake nada tsohon mai rikon kwarya sakataren gwamnati na lokacin tsohon gwamna Gaidam, Alhaji Baba Mallam Wali a matsayin sakataren gwamnati kamar yanda sanarwar gidan gwamnatin jihar ta fitar.

A Akwa’ibom, Emmanuel Ekuwem ne gwamnan jihar, Udom Emmanuel ya sake nadawa a matsayin sakataren gwamnati. Haka kuma, ya sake nada Mista Ekerete Udoh a matsayin mai ba da shawara na mussamman    kuma shugaban sashen labarai.

A Kano, gwamna Abdullahi Ganduje ya sake nada Alhaji Usman Alhajo a kujerar sakataren gwamnati sai kuma, Alhaji Shehu Mu’azu babban akawun jihar. Ganduje ya yaba da irin kwazon da su ka nuna a lokacin mulkin zangon su na farko.

To sai dai, a bangaren gwamnatin tarayya, har yanzu bai nada kowa ba. Buharin ya bar Najeriya zuwa Saudiya awa 24 bayan rantsar da shi a daidai lokacin da ake ta rade-radin ko zai tafi da wasu mukarabban sa ne ko zai yi canji.

A lokacin zaman karshen  da majalisar zartarwarsa, Buhari ya umurci dukkan ministoci da masu sauran mukamai su yi murabus, to sai dai, wasu daga cikin su kamar sakataren gwamnati, Boss Mustapha, an gansu tare da shugaban kasar a daren walimar ranar rantsarwa.

A shekarar 2015 dai, Buhari ya dauki lokaci bai nada shugaban ma’aikata, masu magana da yawunsa da sauran wasu manyan mukamai ba. Sai bayan wata shida da fara mulkinsa ne ya nada ministocin sa.

Wani mai sharhin labarai,  Muhammad Aliyu, a zantawar sa da ‘yan jarida ya bayyana bukatuwar saurin nada mukamai a wannan karon ba tare da jinkiri ba.

Mai sharhin, ya bayyana mamakinsa da jin cewa Buharin ya yi tafiya ba tare da nada kowa ba. Inda ya bashi shawara da ya yi koyi da shugaban kasar Africa ta kudu, Cyril Ramaphosa wanda ya nada mukarrabansa kwanaki kadan bayan nada sa.

Exit mobile version