Connect with us

LABARAI

Wasu Gwamnonin Arewa Da Shugabannin Tsaro Sun Gana Kan Sha’anin Tsaro

Published

on

Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya jagoranci wasu shugabannin hukumomin tsaro na kasar nan a inda suke tattaunawa da gwamnonin arewacin kasar nan a kan tabarbarewar harkokin tsaro a Jihohin na su.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ne ya bayyana hakan ga wakilinmu a daren ranar Litinin.

Matawalle ya kuma ce babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, yana cikin wadanda suke halartar taron.

An gudanar da taron ne a ranar Litinin.

In dai ba a manta ba, a bayan ganawar Monguno da shugaban kasa Buhari da shugabannin hukumomin tsaro na kasa a makon da ya gabata, ya shaida wa manema labarai cewa an dora masa alhakin ganawa da gwamnonin domin samo hanyar kawo karshen matsalolin tsaron da suke fuskantar kasar nan.

Matawalle ya ce dalilin zuwan sa fadar shugaban kasa shi ne domin ya gana da shugaban ma’aikata na fadar ta shugaban kasa, Ibrahim Gambari, a kan matsalar.

Ya ce, “Mun tattauna sosai a kan matsalar tabarbarewar tsaron a arewacin Nijeroya,ba ma a Jihar Zamfara kadai ba.

A yau kuma Litinin mun zauna da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro tare da gwamnonin arewacin Nijeriya da babban sufeton ‘yan sanda na kas da Sauran shugabannin hukumomin tsaro na kasa.

“Mun tattauna sosai a kan matsalolin tsaron, sai shugaban ma’aikatn fadar shugaban kasan ya gayyace ni domin na sanar da shi matsalolin tsaron da suke addaban Jihata, wanda kuma abin da na yi kenan.

“Mun tattauna a kansa, mun kuma fahimci inda muka dosa. Gwamnatin Jihar Zamfara da hukumomin tsaro suna bakin kokarinsu domin tabbatar da magance matsalolin tsaron.

Gwamnan ya bayar da shwarar daukanta da zafi da kuma daukanta da lalama a matsayinn hanyoyin magance matsalar tsaron.

“Akwai wasu ‘yan bindigar da suka tuba wadanda a yanzun haka suke neman zaman lafiya, muna yin amfani da su, sannan wadanda suka ki da a tattauna da su muna kan fafatawa da su,” in ji Matawalle.

Hakanan, babban hafsan tsaro na kasa, Janar Gabriel Olonisakin, ya zauna tare da shugabannin rundunonin tsaro da jami’an binciken sirri dangane da yanayin tsaron a kasar nan.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai babban hafsan Sojin kasa na kasar nan, Laftana Janar Tukur Buratai, babban hafsan Sojin ruwa na kasar nan, bice Admiral Ibok-Ete Ibas, babban hafsanSojin sama na kasar nan, Air Marshall Sadikue Abubakar da sufeton ‘yan sanda na kasa, Mohammed Adamu, da sauransu.

Advertisement

labarai