Kwanan baya, masu aikin jiyya fiye da dari, na cibiyar kiwon lafiya ta Stanford dake jihar California, sun nuna matukar rashin jin dadin su, bisa yadda shirin yin allurar rigakafin COVID-19 da cibiyar ta gabatar, bai hada da su, da suke yakar cutar ba.
Bisa labarin da kafar BBC ta fitar, masu aikin jiyya wadanda suke aiki a dakin masu bukatar gaggawa da ICU na cibiyar, suna ganin cewa, sunansu ba sa cikin takardar wadanda za su riga sauran mutanen samun allurar rigakafi, a maimakon haka, wasu likitoci da ba sa aiki a fagen-daga, suna cikin wannan takarda, hakan ya sa, wadannan jami’an lafiya nuna matukar rashin jin dadi.
Game da wannan batu, cibiyar ta nuna cewa, akwai kuskure a cikin wannan shiri, wanda ya dace kuma a gyara shi nan da nan. (Amina Xu)
Kyautata Alakar Sin Da Amurka Zai Taimakawa Gwamnatin Biden Wajen Shawo Kan Manyan Kalubale
Kamar yadda muka sani, shugaban Amurka na 46 Joe Biden,...