Wasu Jerin Garuruwa Da Suka Fi Dadewa A Duniya

Garuruwa

A kwai garurwa a cikin wasu kasashe a fadin duniya da suka fi dadewa, kuma har ya zuwa yau suna nan kamar kullum, wadanda suka ga zamanoni da dama. Gari na farko shi ne Baranasi, wanda ya a kasar Indiya, garin dai yana dauke da dunbin tarihi, an kiyasta tsawon shekarun wannan garin ya haura shekaru 5,000.

Sai gari na biyu Cadiz, a kasar Sipaniya, wanda akwai mutane da suka zauna a garin tun shekara 1,100 da suka wuce tun kafin zuwan Annabi Isa (AS). Garin shi ma yana da dumbin tarhi, inda jinsin Romawa suka zauna tun a karni na 18. Na uku kuwa shi ne garin Thebes, na kasar Girka, shi kuwa wannan mutane suna zaune a cikinsa sama da shekaru 1,400 da suka wuce kamin zuwan Annabi Isa (AS), yanzu dai garin ya zama kamar wata kasuwa. Gari na hudu kuwa shi ne, Larnaca, a kasar Cyprus, shi dai garin mutane da dama daga wasu fadin duniya su kan ziyarci garin don ganin ire-iren gine-ginen da suke da shi masu matukar kayatarwa, shi ma dai garin yana da shekaru 1,400 da suka wace.

Gari na biyar kuwa shi ne Athens, shi ma dai yana kasar Girka, wannan garin na daya daga cikin garuruwa da aka yanke wa wayewa cibi, domin kuwa ya zama wata mahada ta jinsin mutane daban-daban a fadin duniya, kuma an kiyasta shekarun garin, inda marubuta tarihi suka ce ya rayu sama da shekaru 7,000. Gari na shida kuwa shi ne Balkh, shi kuma yana nan a kasar Afghanistan, shi ma dai gari ne da aka kiyasta shekarun sa cewa da cewa sun haura 2,500 tun kafin bayyanar Annabi Isa AS.

Haka garin Kirkuk, da ke kasar Irak, shi ne na bakwai, wannan gari ya rayu kimanin sama da shekaru 2,200 kafin zuwan Annabi Isa (AS), mutane suka fara zama a wannan garin, har ya zuwa yau akwai gine-hgine da suka haura shekara 5,000 a garin, wanda yanzu haka shi ne babban birni da ke da arzikin mai a kasar ta Iraki.

Gari na takwas kuwa Arbil, duk a kasar Iraki, shi ma ya zauna tsawon sama da shekaru 2,300. Na tara kuwa shi ne Tyre, da ke kasar Lebanon, da ke da tarihin mutane da suka zauna a garin sama da shekaru 2,750 kafin bayyanar Annabi Isa.

Gari na 10 shi ne, Jerusalem, a yankin kasashen Larabawa, shi dai wannan garin yana da dumbin tarihi, a cikin garin ne babban Masallacin Al-Aksa yake, Masallaci na uku a daraja a duniya, sai kuma Chocin Sepulcher, mutane sun fara zama a wannan garin tun a shekarar 2,800 da suka gabata kafin zuwan Annabi Isa (AS).

Exit mobile version