Connect with us

JAKAR MAGORI

Wasu Maza Biyu Sun Kashe Kansu A Neja

Published

on

Maza biyu masu matsakaitan shekaru sun kashe kansu a karamar Hukumar Rijau da ke Jihar Neja.

Lamarin ya zamo shi ne irinsa na 13 da ya faru a lokuta daban-daban cikin watanni biyu da su ka gabata.

Mutanen biyu da suka mutu, wadanda aka bayyana sunayensu Barde Swashi da Jibrin Dakarkari, sun rataye kansu a jikin bishiya kuma ba su ba da labarin dalilin da ya sa suka kashe kansu ba.

A game da Barde Swashi, an iske gawar tasa a rataye jikin reshen bishiyar mangoro a cikin gonar da ke cikin garin Darangi da ke cikin Rijau a safiyar ranar Juma’a.

Iyalan gidansa sun ce ya bar gida ba tare da wani bayani game da inda ya nufa ba, suna masu cewa ba su taba lura da cewa yana fuskantar wata matsala ba wacce za ta sa shi ya kashe kansa.

“A wannan ranar mai ban tsoro, bai taba nuna wani sabon abu ba kuma ba mu taba tsammanin zai rataye kansa a gonarsa ba.

“Don haka abin mamaki ne a gare mu yayin da muka samu labari mai muni da na cewa wani dattijo mai tsaka-tsakin shekaru an ga gawarsa a rataye jikin reshen bishiyar mangwaro cikin wata gona, kuma da mu ka isa gona, mun gano gawarsa ta mu ce,” a cewar wani dan gidan.

Jibrin Dakarkari, wanda ke tsakiyar shekara ta 60 daga yankin Dukku ya koka wa makwabta cewa ba zai iya cigaba da rayuwa ba tare da samun wani aikin tanki da yake nena wanda ya ke ganin da shi ne zai samu abin da zai rika ciyar da iyalinsa ba. Amma makotansa ba su tunanin hakan zai iya janyowa har ya kai ga kashe kansa ba.

An samu gawar Jibrin rataye jikin wata bishiya da ke bayan gidansa da sanyin safiyar ranar Laraba.

daya daga cikin makwabtansa, wanda ya yi magana da manema labarai ya ce: “Ba mu taba tunanin zai kashe kansa ba da wannan maganar da ya yi duk da cewa mun gamsu da cewa komai zai yi daidai.”

Mazauna karamar Hukumar Rijau sun damu matuka game da yawaitar kashe-kashen mutane musamman a tsakanin tsofaffi tsakanin shekaru 55 zuwa 60 kuma sun yi kira ga gwamnati da ta fara shirye-shiryen wayar da kai wanda zai sake karfafawa mutane gwiwa kan su nisanci kashe kansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: