Wasu Na Neman Bata Sunan Yankin Xinjiang Na Sin Babu Gaira Babu Dalili

Daga CRI Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa Jumma’ar nan cewa, wasu makiyan kasar Sin na yada jita-jita da karairayi game da yankin Xinjiang na kasar Sin ba kai ba gindi.

Zhao Lijian ya kara da cewa, bangaren Burtaniya ya rufe idonsa game da batutuwansa da suka shafi kare hakkin bil-Adama, amma yake kokarin zama “malami” tare da sukar yanayin kare hakkin dan-Adama na sauran kasasahe.

Wannan ya fito da munafurcinta da yadda take nuna fuska biyu a fili.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version