Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kashe Masunta 31 A Baga

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe wasu masunta 31 a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce wannan hari na nuna cewa har yanzu ‘yan  kungiyar na kai hare-hare masu muni da kashe mutane a yankin tafkin tekun Chadi.

Gwamna Shettima ya ce har yanzu jami’an tsaro ba su tabatar da rahoton harin ba, yayin da y ace, shi ma ya samu kiran waya ne daga wasu da ke yankin, wadanda suka shaida lamarin, suka kuma tabbatar masa da aukuwar harin.

 

 

Exit mobile version