Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Bayern munchen, Uli Hoennes ya bayyana cewa wasu yan wasan kungiyar ne suka nuna basa tare da carlo ancelotti wanda kungiyar ta kora asatin daya gabata.
Hoennes yace, kungiyar koda yaushe tana duba bukatar yan wasa kuma wasu yan wasan kungiyar basa tare da mai koyarwar wanda hakan yasa dole sai sun nemi masala.
Sai dai kuma mataimakin shugaban kungiyar ya bayyana cewa sun yanke hukuncin korar anceloti ne saboda kungiyar bata buga abinda yakamata wanda hakan yasa yake ganin suna bukatar canji.
Sai dai Hoennes yace wasu yan wasa biyar a kungiyar sune suka juyawa mai koyarwar baya saboda haka suka dauki wannan mataki.