Mai koyar da yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta real Madrid, Mauricio Pochettino, ɗan ƙasar Argentina yace wataƙila ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Harry Kane, ɗan ƙasar ingila zai iya buga wani bangare na wasan da ƙungiyar za ta fafata da Real Madrid.
Kane, mai shekaru 24 yasamu rauni ne a karawar da ƙungiyar tayi da Liɓerpool mako biyu daya gabata wasan da ƙungiyar ta lallasa Liɓerpool ɗin da ci 4-1 inda kane ɗin yazura ƙwallaye biyu a wasan
Pochettino yace, dole sai sun kula sosai sun duba lafiyar ɗan wasan domin ba za su yi gangancin yin amfani dashi a wasa ba kuma nan gaba a zo a sake samun sabuwar matsala.
Ya ci gaba da cewa ƙungiyarsa tana buga kofuna daban daban saboda haka dole sai sun kula da lafiyar kowanne ɗan wasa domin yanzu aka fara wasanni kuma sai da lafiya ɗan wasa zai iya buga wasa.
Tottenham dai itace a matsayi na uku a kan teburin firimiya maki uku tsakaninta da Manchester united wadda take matsayi na biyu sannan sai Manchester city wadda take matsayi na daya kuma ta bawa Tottenham ɗin maki takwas.
A ranar Laraba ne dai Tottenham za ta karɓi baƙwancin real Madrid a filin wasa na Wembley dake Birnin Landan a wasan zagaye na hudu kuma Tottenham ɗin ce a matsayi na daya a rukunin sai real Madrid ɗin wadda take binta a baya.