Daga Abba Ibrahim Wada
Rahotanni sun bayyana cewa wataƙila mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino ya maye gurbin Zinedine Zidane a real Madrid idan har zidane ɗin yabar ƙungiyar.
Zidane dai ya lashe kofuna 7 a real Madrid cikin shekara daya da rabi da yayi a a ƙungiyar bayan daya karbi ƙungiyar daga hannun Rafael Benitez.
Shugabannin ƙungiyar dai ta real Madrid suna tsoron zidane ɗin zai iya barin ƙungiyar kowanne lokaci daga yanzu bayan da ake rade-raɗin cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG tana zawarcin mai koyarwar, wanda ɗan asalin ƙasar faransa ne.
Mai koyarwar, ya taba koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Espanyol a shekarun baya kafin ya karbi Tottenham ɗin inda ya jagoranci ƙungiyar takai mataki na biyu dana uku a gasar firimiya cikin shekaru biyu.