Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin ƙwace gidaje biyu, tare da motocin alfarma guda biyu na tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke.
BBC ta rawaito cewa, wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Tuwita hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC ta ce gidan tsohuwar ministar mai lamba 1854 a kan titin Mohammed Mahashir, da kuma dayan mai lam 6 Aso Drive, na a unguwannin Maitama da Asokoro da ke Abuja babban birnin kasar.
Rahoto
Hukumar ta ce darajar kuɗin gida dayan ta kai dala 2,674,418, dayan kuma darajarsa ta kai naira miliyan 380,000,000.