Wata Kungiya Ta Yi Gangamin Fadakarwa Kan Allurar Rigakafi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Wata gamayyar ƙungiya mai suna ‘Bauchi South Youth Coalition’ da haɗin guiwar ‘Bella Foundation’ da haɗin guiwar a ƙarƙashin hukumar lafiya ta duniya ‘WHO’ sun kaddamar da gangamin faɗakar da jama’a kan muhimmacinsa yin allurer rigafi ga yara ƙananan, haɗe kuma da nemo rahoton yankunan da suke da ƙarancin wayewa kan allurer rigafin.

Wannan shirin dai yana gudana ne a ƙarƙashin hukumar lafita ta duniya wato ‘WHO’ inda gamayyar ƙungiyar suka zundumar faɗakar da jama’a kan muhimmancin allurar na rigakafi. Comr. Daure Daɓid Yankshi wanda shi ne ya jagorancin gangamin faɗakar da jama’an ya bayyana cewar sun fito ne domin bayyana wa al’umma muhimmancin da ke cikin wannan allura gami da tattara bayanan yankunan da suke da tangarɗar fahimtar muhimmancin allurer.

“Mun fara wannan shirin ne domin kaddamar a asibitin Tashan Babiye da kuma faɗakar da mata musamman masu ciki kan muhimmancin allurer rigakafin. Haka kuma mun je unguwar Rariya domin faɗakar da jama’a, mun haɗu da ma’aikatar da suke wannan aikin na allura”.

Ya ƙara da cewa su ba nasu bane yin allurar amma suna kan faɗakar da jama’an jihar Bauchi muhimmancin da akwai “muna kuma naɗan matsalolin da yankuna suke da shi domin gabatar da rahoton ga hukumar lafiya na duniya, musamman inda suke ƙin yin wannan allurar, kafin nan muna gabatar da shawarori”. A cewarsa

Ya bayyana cewar aikin nasu zai ci gaba da gudunawa ne har su kammala karaɗe manya da kuma ƙananan unguwanin da suke faɗin jihar ta Bauchi.

A zantawarmu da shi, Mai unguwar Gwallaga, wanda kuma shi ne shugaban masu unguwanin jihar Alhaji Dan Dada Amadu ya bayyana cewar a shiye suke su mara baya wa dukkanin ƙungiyoyin da suke faɗi tashin taimaka wa al’umma musamman kan irin wannan aiyukan masu alfanu “Ina ƙira ga al’uman jihar Bauchi da su mara baya ɗari bisa ɗari wajen kariyar lafiyarmu, wannan irin faɗakarwa da kuma rigakafin da ake yi wa al’umma abu ne mai kyau sosai, muna son al’umma su kasance masu cikakken lafiya, a bisa haka wajibi ne jama’a su mara baya domin samun lafiya sosai”. In ji mai unguwar a lokacin da masu gangamin suka isa unguwarsa domin faɗakar da jama’an unguwar.

Mai unguwar ya bayyana cewar unguwarsa ta Gwallaga mutane ne masu amsar shawarorin mahukunta da kuma ƙungiyoyi masu taimaka wa jama’a “daman mu a kullum muna son mu samu jama’a su zo da kyakkyawar tunani don haka muke shirye mu mara baya wa irin waɗannan ƙungiyoyi, domin hakan zai tada mu daga barci”. A cewarsa

Exit mobile version