Chen Miao tana aiki a wani sashen masana’antar sarrafa fansira dake kauyen Shizilu na garin Matou dake yankin Jin’an na lardin Anhui na kasar Sin, yanzu, ita ce shugabar wannan sashe, amma a baya, ta shafe shekaru da dama tana fama da talauci.
A shekarar 2013 ita da mai gidanta, sun dawo garinsu domin kula da mahaifinsu, bayan ya kamu da cutar sankara. Kuma, kudin jinyar mahaifin nasu ya dame ta da mai gidanta kwarai da gaske. Abin bakin ciki shi ne, mai gidanta ya gamu da hadarin mota, har ba ya iya aiki. Chen Miao ta ce, a lokacin, ba ta san yadda za ta yi ba.
Shi ya sa, a shekarar 2014, an shigar da iyalinta cikin jerin masu fama da talauci.
Sa’an nan, wata abokiyarta ta gaya mata cewa, ana neman ma’aikata a wata masana’antar sarrafa fensira, sabo da haka, Chen Miao ta je masana’antar domin neman aiki.
Kafin mahaifinta ya kamu cutar sankara, ita da mai gidanta suna aiki a waje, yanzu, Chen Miao tana aiki a garinta, ban da samun kudin shiga, abu mafi muhimmanci shi ne, tana kusa da gida, ta yadda za ta iya kula da iyalinta. Kuma, masana’antar da take aiki, ta ba ta lokacin zuwa asibiti domin kula da mahaifin nata.
Lamarin da ya sa, a shekarar 2015, Chen Miao da iyalinta sun cimma nasarar kawar da talauci, kuma, a shekarar 2017, an nada ta shugabar wani sashen masana’antar sarrafa fensira, saboda kokarinta wajen gudanar da ayyukanta.
Bayan da mai gidanta ya warke, shi ma ya fara aikin sufuri, inda a ko wace shekara, yana samun kudin shiga yuan dubu 60. Zaman rayuwarsu na ci gaba da samun kyautatuwa.
A halin yanzu, an kafa sassan taimakawa masu fama da talauci guda 8 a cikin masana’antar, gaba daya, akwai mutane kimanin 260 dake aiki a masana’antar, kuma, ko wanensu yana samun kudin shiga yuan dubu 10 a ko wace shekara. Daya bayan daya, an taimaki mutane 148 wadanda suke aiki a wannan masana’anta wajen fita daga matsalar talauci,. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)