Wata mata mai suna Bilkisu Abubakar ta yanke jiki ta fadi ta kuma mutubayan cece-kucen da ta yi da kishiyarta mai suna Hajara Abubakar.
Dukkanin su matan Abubakar ne da take zama a kauyen Jiramo dake karamar hukumar Takai a cikin jihar Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da afkuwar lamarin, unda ya ce, lamarin ya auku ne a ranar Larabar da ta gabata da misalin karfe 10 na dare.
Ya ci gaba da cewa, Dagacin kauyen Fajewa, Alhaji Ya’u Hamza ne ya kawo rahoton ga rundunar tare da kishiyar da ake zargi Hajara..
A karshe ya ce, wadda ake zargin sun samu rashin fahimta, inda hakan ya janyo suka kaure da dada hakan kuma ya janyo mutuwar Bilkisu an kuma ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki na Babban Asibitin jihar.