Wata Mata Ta Yi Wuf Ta Aure Saurayin Diyarta A Kano
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wata Mata Ta Yi Wuf Ta Aure Saurayin Diyarta A Kano

bySulaiman
3 years ago
Mata

Wani lamari mai kamar wasan kwaikwayo da ya faru a karamar hukumar Rano ta jihar Kano bayan wata mata mai suna Malama Khadija ta kashe aurenta ta auri saurayin ‘yarta. 

Lamarin ya faru ne bayan diyar mai suna A’isha ta ki amincewa da mai neman aurenta, inda mahaifiyar ta ce, auran mai neman ‘yarta bai haramta ba a Musulunci.

  • An Gudanar Da Baje Kolin Hotunan Tashar Samaniya Ta Sin

Tun da farko dai ‘yan uwan matar sun shaida wa gidan rediyon Freedom cewa suna zargin kwamandan Hisbah na karamar hukumar Rano da aurar da ‘yarsu ba tare da izininsu ba, kuma ba su ma san inda take ba.

Sai dai kuma da take magana da Freedom Radio, Malama Khadija ta ce tana cikin koshin lafiya kuma tana zaune lafiya da sabon mijin nata.

Ta bayyana cewa bayan da ta fahimci cewa ’yarta ta yanke shawarar ba za ta auri mutumin ba, sai ta ji bai kamata su biyu su rasa shi ba, don haka ta yanke shawarar auran mutumin. Ta kuma kara da cewa itama tana da kyau kamar ‘yarta.

Ta ce, “Ban yi auran cikin jahilci ba. Na tuntubi malamai suka ce hakan ba haramun ba ne. Da na tuntubi mutumin kan aure na, ya amince shi amma iyayena da ’yan uwana sun ki amincewa da auran. Hakan ne ya sa na yanke shawarar zuwa Hisbah su daura mana aure wanda yanzu haka, muna cikin farin ciki.”

Kawun Malama Khadija, Abdullahi Musa Rano, ya ce sun ki yarda ta auri mutumin ne sabida da gangan ta kashe aurenta na farko domin ta auri mai neman ‘yarta.

Ya bayyana cewa, “Ta matsa wa mijinta ya sake ta don kawai ta auri wannan sabon mijin na ta. Ba za mu yarda da wannan abin kunyar ba a cikin danginmu. Wannan shine dalilin da ya sa muka ki hada su da aure. Ba mu ji dadin abin da Hisbah ta yi ba, kuma muna ba da rahoton neman ‘yar mu. Muna son babban kwamanda da gwamnatin jihar su shiga cikin wannan lamarin.”

Da aka tuntubi kwamandan Hisbah, Ustaz Nura Rano, ya ce hukumar ta jiha ce kadai ke da damar yin magana kan lamarin.

Da aka tuntubi babban kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Harun Ibn-Sina, ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Daga Daily trust

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
Labarai

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Next Post
Dino Melaye Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Taron PDP Yayin Da Yake Zolayar Tinubu

Dino Melaye Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Taron PDP Yayin Da Yake Zolayar Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version