Umar A Hunkuyi" />

Wata Qaramar Hukuma A Kaduna Ta Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi

Karamar Hukumar Ikara, a Jihar Kaduna ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na naira 30,000 ga ma’aikatan ta tun daga ranar 4 ga watan Oktoba, 2019.

Shugaban karamar hukumar, Hon. Ibrahim Salihu Sadik, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mai taimaka ma sa na musamman a kan harkokin yada labarai, Abdulmajid Hussaini, ya sanya wa hannu.

Ya ce ya yi hakan ne domin karfafa aniyar gwamnan Jihar Nasiru El-Rufai, a bisa kokarin da yake yi na kyautata wa ma’aikatan gwamnatin Jihar ta yanda za su gudanar da ingantaccen aiki.

Shugaban a cewar sanarwar, ta bayar da tabbacin yin gaskiya da adalci a matsayin abin da gwamnatin za ta yi dogaro da shi.

Ya kuma bukaci ma’aikatan da su nuna kwazo, kwarewa da kuma dagewa a kan ayyukan na su, sai ya yi alkawarin inganta dukkanin abin da ya shafi jin dadin ma’aikatan.

 

Exit mobile version