Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da ake ce-ce-ku-ce a kansa ya sake garzayawa Babbar Kotun Tarayya da ke Kano inda ya maka Gwamnatin Jihar Kano da rundunar ‘yan sanda a kotu, yana neman a bi masa hakki na take masa ‘yancin dan Adam.
A ranar Laraba ne malamin ya kai karar yana so a hana gwamnatin jihar da ‘yan sanda ci gaba da rufe masallacinsa da kuma hana shi wa’azi.
Wadanda malamin yake kara sun hada da Gwamntain Jihar Kano, da Babban Jami’inta na Shari’a da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar.
Sai dai kuma, kotun bias shugabancin Mai Shari’a Lewis Allagoa ta dage saurarar karar zuwa 18 ga Fabarairun nan, inda ta umurci a aika da takardar sammaci ga wadanda ake kara kafin ranar da za a sake zama a kan batun.
A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar ta Kano ta hana Abduljabbar wa’azi bisa abin da ta kwatanta da rashin ta ido a cikin wa’azozinsa. Wakazalika ta rufe masallacinsa nan take da kuma haramta wa kafafen yada labarai sanya hudubobi da wa’azozinsa.
A karar da malamin ya shigar a gaban kotun, ya kalubalanci matakin gwamnatin, inda ya kafe kai da fata cewa kan cewa an danne masa ‘yancin fadar albarkacin baki, kai-komo da tara taro na zaman lafiya.
Fulani Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne –Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce...