Idris Aliyu Daudawa" />

Wata Sabuwa: Tafiya A Hankali Na Kawo Saurin Tsufa

Irin yadda mutane ke tafiya a lokacin da suka zarce shekaru 40 alama ce wadda take   cewar ga irin yadda kwakwalwarsu da kuma jikin su yake tsufa, kamar yadda masu binciken kimiyya su ka gano.

Masanan sun yi amfani ne da wata manhaja da ke nuna yadda matakan tsufa su ke.

Ba kawai jikin masu tafiya a hankali ke nuna saurin tsufa ba, har ma da fuskokinsu kan takure kuma da ma suna da karamar kwakwalwa.

Kungiyar wadda ta kasa da kasa ce wadda kuma ita ce ta gudanar da shi wannan bincike ta bayyana matukar mamaki dangane da abin da ta gano. yawancin likitoci kan yi amfani ne da manhajar ‘gait speed’ domin duba lafiyar jama’a musamman tsofaffi da suka wuce shekaru 65,wurin gano karfin jijiyoyinsu da lafiyar huhunsu da kuma kashin baya da kuma idonsu.

Bugu da kari kuma tafiya a hankali ga tsofaffi na da alaka da cutar mantuwa.

Binciken ya yi amfani ne da mutane 1,000 a New Zealand da aka haifa a shekarar 1970, inda aka gudanar da bincike kan yanayin jikinsu da kwakwalwarsu tare da yin gwaji akan yadda suke fahimtar abubuwa duk bayan wasu shekaru tun a lokacin kuruciyarsu.

Binciken dai ya tabbatar da cewa tafiya a hankali alama ce ta wata cuta da ta dade a jikin mutun wadda kuma ta kama shi ne shekaru da masu yawa kafin tsufansa, a cewar Farfesa Terrie E Moffitt,wanda ke jagorantar binciken daga Jami’ar King’s College London da kuma Jami’ar Duke da ta ke Amurka.

Ko a shekaru na 45 an gano cewar da akwai bambanci sosai bayan lura da cewa masu tafiya da sauri kan yi tafiyar mita biyu a cikin dakika daya ba tare da sun yi shessheka ba.

A takaice dai masu tafiya a hankali sun nuna alamun ‘tsufa da wuri’ yayin da huhunsu da hakoransu da kuma kwayoyin halittarsu ke samun nakasu ba kamar na sauran takwarorinsu ba da su ke tafiya da sauri ba.

Bayan da a ka maida hankali sosai akan yin shi binciken sai kuma aka gano cewar kwakwalwar masu tafiya a hankali ta na tsufa da wuri.

Har ila yau masu binciken sun yi nasarar gano yanayin saurin tafiyar masu shekaru 45 ta yin amfani da wadansu dabaru daban-daban tun suna ‘yan shekaru uku.

Wannan yana nuna cewar su kananan yara da ke girma suna kuma da matsalar tafiya a hankali suna iya haduwa da matsalar rashin karfin kwakwalwa da kashi 12 idan aka kwatanta da takwarorinsu da ke tafiya da sauri bayan sun shekara 40 ko fiye da haka.

 

Alakar Tafiya A Hankali Da Tsarin Rayuwa:

Sai dai wata kungiyar masu bincike ita kuma ta gano cewar bambancin lafiya da karfin kwakwalwa na da alaka da irin yadda yara ke samun kula da lafiya tun bayan haihuwarsu.

Sun kuma bayyana cewa tun a lokacin za a iya fahimtar wanda zai iya tsufa da cikakkar lafiya.

Gano irin saurin da jama’a ke yi a lokacin da suke tafiya tun lokacin kuruciyarsu ita ce babbar hanyar magance wannan matsala.

Akwai wasu hanyoyin kawar da wannan cuta da suka hada da cin abinci maras kitse sosai, da kuma amfani da kwayar ‘metformin’ duk kuwa da yake har yanzun da ba a kammala bincike maganin ba.

Akwai kuma bukatar jama’a su kula da lafiyar kwakwalwa da kuma ta jiki tare da sauya yanayin tsarin rayuwarsu tun suna da kuruciya da cikakkar lafiyar samun yin hakan.

 

 

Exit mobile version