Connect with us

LABARAI

Wata Sabuwa: Yadda PDP Ta Rushe Shugabancinta A Kano

Published

on

Majalisar koli (NWC) ta babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta tsige dukkanin jagororin jam’iyyar na jihar Kano, tsigewar ta kuma fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labarai, wacce kakakin jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hanu hadi da raba wa ‘yan jarida a ranar Juma’ar nan.
Mr Ologbondiyan ya shaida cewar an dauki wannan matakin ne biyo bayan zaman da majalisar NWC ta yi a ranar Alhamis, inda su ka amince da tsige dukkanin shugabanin jam’iyyar a matakin jihar ta Kano.
Ya ce, baya ga nan, tuni majalisar kolin ta kuma amince da nada shugabanin riko. “Sannan kuma kwamitin riko tuni mu ka kafa su a jihar Kano. Cikakken bayani kan shugabanin rikon za mu sake wa jama’a nan gaba kadan da kuma cikakken dalilanmu,” in ji jam’iyyar.
Ya cigaba da cewa, “Dukkanin jam’iyyar PDP a jihar Kano da fadin kasar nan su dauki wannan matsayar kamar yadda aka dauka.”
Babu wani cikakken bayani da jam’iyyar ta yi kawo yanzu dangane da wannan matsayar nata, sai dai binciken LEADERSHIP A YAU LAHADI ya na nuni da cewar kila tsigewar ta na da nasaba da dirkaniyar da ke jibge na shigar wasu kusoshi cikin jam’iyyar a jihar, kamar tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso.
Bincikenmu ya gano cewar matakin kamar wani yunkuri ne na mika wa Sanata Kwankwaso jagorancin jam’iyyar ta PDP a jihar a bisa tafin hannunsa, wanda kuma hakan zai samu suka daga sauran kusoshi a jam’iyyar kamar su Malam Ibrahim Shekarau, Ambasada Aminu Wali da sauransu.
Sai dai wasu kusoshin jam’iyyar su na ganin wannan matakin a matsayin wata hanyar da ka iya jefa jam’iyyar ta PDP cikin sabon rikici, domin sauran bangarorin da ke cikin jam’iyyar ba lallai su gamsu da wannan matakin ba.
“Da ma tun lokacin da Sanata Kwankwaso ya shiga jam’iyyar a ka fara samun rikici kan yunkurin kwace shugabancin jam’iyyar a jihar,” in ji daya daga cikin kusoshin jam’iyyar. Ya kara da cewa tuni shugabannin jam’iyyar na Kano su ka samu umarnin kotu da ya hana rushe shugabancin jam’iyyar a Kano.
A baya ma an samu irin wannan matsala lokacin da Kwankwaso ya koma APC, abin da ya sa Shekarau da magoyansa su ka fice saboda zargin rashin adalci daga shugabannin APC na kasa a lokacin.
A yanzu haka dai bayanai na cewa jagororin jam’iyyar a Kano da su ka hada da shi Shekarau da Wali da kuma Sanata Bello Hayatu Gwarzo sun yi tsayuwar daka cewa ba za su bari a kwace jam’iyyar a mika wa Kwankwaso ba.
Hakan dai na iya zama wani babban kalubale ga jam’iyyar, wanda zai iya rage mata tagomashi a jihar.
Jihar Kano dai daya ce daga ciki manyan jahohin da su ke da mafiya yawan mutane a Arewacin Nijeriya, inda shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya samu mafi yawan kuri’u sama da miliyan 1.9 a zaben 2015.
Wata majiya ta shaida ma na cewa, wannan rikici ka iya kai wa gaban kuliya manta sabo, lamarin da a ke ganin zai iya jaza wa PDP asarar takarar gwamna a jihar, idan wutar ba ta mutu ba har zuwa lokacin zaben 2019, domin takaddama kan wanda ya cancanci ya gudanar da zaben fitar da gwani tsakanin zababbun shugabannin da a ka rushe da kuma kwamitin riko na iya zama babbar gardama mai hatsari ga jam’iyyar a gaban kotu.

Advertisement

labarai