Abba Ibrahim Wada" />

Watakila A Soke Kofin Zakarun Turai Da Europa

NYON, SWITZERLAND - July 22: A general view of the trophy ahead of the UEFA Champions League 2019/20 Third Qualifying Round draw at the UEFA headquarters, The House of European Football on July 22, 2019 in Nyon, Switzerland. (Photo by Harold Cunningham - UEFA/UEFA via Getty Images)

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasashen turai, Eufa, ta ce Watakila a soke gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da ta Europa ta bana idan ba a shawo kan annobar cutar coronabirus zuwa watan Satumba ba kamar yadda shugaban hukumar, Aledandre Ceferin ya bayyana.

Shugaban hukumar, Aleksander Ceferin ne ya bayyana haka, sai dai ya ce gwara a karasa wasannin ba tare da ‘yan kallo ba maimakon a soke kakar bana gaba daya saboda hakan zai haifar da asara sosai.

Kawo yanzu dai an dakatar da dukkan wasannin Champions League da na Europa sakamakon tsoron yada coronabirus kuma banda gasar ta nahiyar turai an dakatar da dukkan wani wasa a duniya.

Kungiyoyin Manchester City da Chelsea na buga gasar cin kofin zakarun turai na Champions League, ya yin da su kuma kungiyoyin Manchester United da Wolberhampton ke fafatawa a Europa League.

Tuni Uefa ta dakatar da wasannin karshe na cin kofin Champions League na maza da na mata da na Europa da ya kamata a karkare a cikin watan Mayu sai dai kamar yadda shugaban ya bayyana nan gaba kadan zasu sake zama domin saka sabuwar rana.

A kasar Ingil ma an dakatar da wasannin Firimiyar Ingila da gasar Laliga ta kasar Sipaniya da kuma wasannin da ake bugawa na kwallon kafa da wadanda bana kwallon kafa ba a duniya duka saboda Coronavirus.

Exit mobile version