Connect with us

WASANNI

Watakila Ba Za A Sake Dakatar Da Ronaldo Ba

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa watakila hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai bazata sake dakatar da dan wasan Jubentus ba Cristiano Ronaldo daga buga wasanni uku bayan an bawa dan wasan jan kati a wasan da Jubentus ta doke Balencia a gasar cin kofin zakarun turai.

An bawa dan wasa Ronaldo jan kati ne a daidai minti na 30 da fara wasan bayan da alkalin wasa ya kama dan wasan yaja gashin dan wasan baya na Balencia, Jeison Murillo a wasan da Jubentus din tasamun nasara daci 2-0.

Sai dai Ronaldo dole bazai buga wasan da kungiyarsa zata buga na gaba ba da kungiyar Young Boys kamar yadda doka take ga duk dan wasan da aka bawa jan kati amma zai iya buga wasan da Jubentus zata buga da tsohuwar kungiyarsa Manchester Ujited.

Da farko dai an yi tunanin hukumar kwallon ta nahiyar turai zata sake duba katin korar da aka bawa Ronaldo da niyar idan aka tabbatar yayi abin da ganganne za’a sake bashi karin wasanni biyu.

Sai dai hukumar kula da kwallon ta nahiyar turai zata yanke hukunci a ranar Alhamis mai zuwa inda zata bayyana matsayinta akan jan katin da aka bawa Ronaldo tare da la’akari da rahoton da alkalin wasa Felid Bryd, dan kasar Holland zai kai akan abinda yafaru.

Jubentus dai ta fito acikin rukunin daya hada da Manchester United da Young Boys ‘yan kasar Switzerland sai kuma Balencia ta kasar Sipaniya sai dai kawo yanzu Manchester United ce ta daya acikin rukunin bayan tasamu nasara har gidan Young Boys daci uku babu ko daya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: