Abba Ibrahim Wada" />

Watakila Ba Za Mu Sake Sayen Dan Wasa Ba – Kociyan Barcelona

Mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Enestor Balberde, ya bayyana cewa kawo yanzu yana ganin kungiyarsa bazata sake sayan dan wasa ba a wannan kakar saboda kudaden da suka ware sun kare.

Kociyan ya bayyana hakane bayan da Barcelona ta kammala daukar dan kwallon tawagar Spaniya ta matasa ‘yan kasa da shekara 21, Junior Firpo kan fam miliyan 27.5 kuma dan wasan da Barcelona ta sayo daga Real Betis, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Tuni kuma kungiyar ta Barcelona ta gindaya fam miliyan 183 ga duk wadda take son daukar dan wasan mai shekara 22 idan yarjejeniyarsa bata kare ba a Barca har ila yau Firpo ya buga wasanni 29 a kakar bara, yana kuma daga cikin tawagar Spaniya ta matasa ‘yan shekara 21 da suka lashe kofin nahiyar Turai a cikin watan Yuli.

“Duk da cewa bukatar sayo ‘yan wasa bata karewa amma ina ganin munzo karshen yin duk wani ciniki a wannan kakar saboda irin kudaden da muka kashe wajen sayan manyan ‘yan wasan da a yanzu muke tare dasu” in ji kociyan kungiyar ta Barcelona

A cikin watan Yuli Barcelona ta dauki Antoine Griezman daga Atletico Madrid kan fam miliyan 107  haka kuma Barcelona ta sayo Frenkie de Jong daga Ajad kan fam miliyan 65 da mai tsaron raga Neto daga Balencia da mai tsaron baya Emerson daga Atletico MG ta Brazil.

A ranar Talata Barcelona ta sayar da Malcom ga Zenith St Petersburg kan fam miliyan 36.5, bayan kaka daya da ya yi a kungiyar sai dai har yanzu ana cigaba da danganta kungiyar da tsohon dan wasanta Neymar, wanda yakeson barin PSG zuwa tsohuwar kungiyar tasa sai dai idan har tanason daukar dan wasan sai dai tayi musanye da wasu daga cikin ‘yan wasanta.

Exit mobile version