Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Karim Benzema zai iya rasa wasan da kungiyar zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Atalanta a gasar zakarun Turai bayan da kociyan kungiyar Zinedine Zidane ya tabbatar da cewa dan wasan ya ji rauni ya yin wasan kungiyar na ranar Alhamis.
Benzema bai halarci daukar horo a safiyar Juma’a da Asabar da Lahadi ba, kuma baya cikin tawagar ‘yan wasan da sukayi tattaki ranar Asabar inda suka fafata da kungiyar Real Balladolid a gasar Laliga.
To sai dai, Har yanzu kungiyar ba ta tabbatar da takamaiman irin raunin da dan wasan ya samu ba sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa dan wasan dan asalin kasar Faransa gurdewa yayi a kafarsa ta dama.
‘Bani da tabbacin irin matsalar daya samu amma tabbas ina da tabbacin cewa yaji ciwo kuma likitoci suna ci gaba da kula da lafiyarsa kuma yau yakamata su gayamana matsayin ciwon da kuma tswon lokacin da zai dauka” in ji Zidane
Real Madrid dai na kara fuskantar kalubale a kakar bana, bayan da ‘yan wasanta da dama ke yin jinya kawo yanzu wanda hakan yana daya daga cikin matsalolin da suka addabi kociyan kungiyar.
Real Madrid wadda take rike da gasar La Liga, ba ta kare kofinta na Spanish Super Cup ba a shekarar nan, an kuma yi waje da ita a gasar cin kofin Copa del Rey bayan karamar kungiyar Alcoyano tayi waje da ita.
Yanzu dai ta mayar da hankali ne kan lashe gasar La Liga wanda take ta uku a kan teburin wasannin bana da kuma gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da za ta kara da kungiyar Atalanta a cikin watan nan na Fabrairu.
To sai dai da yawan ‘yan kwallon Real Madrid na fama da jinya da hakan zai iya zama barazana kan kokarin da take na ganin ta tsira da kofi a kakar nan duk da cewa kungiyar ba ta kokari musamman idan tana buga wasa da kana nan kungiyoyi.
A satin daya gabata likitoci suka yi wa kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos tiyata a kafarsa ya kuma bi sawun masu jinya da suka hada da dan wasa Eden Hazard da Rodrygo da Dani Carbajal da Marcelo da kuma matashin dan wasa Fede Balberde.
Sau 38 ‘yan wasan Real Madrid guda 20 suka yi rauni a kakar bana mai cike da kalubale sai dai daman Real Madrid ba ta dauki dan kwallo ba a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021, kuma cutar korona ta kawo tsaiko da ta kai ana buga wasanni da yawa a karamin lokaci.
Real Madrid wadda take ci gaba da fuskantar barazanar rashin nasara za ta fuskanci kalubale a watan Fabrairu, wadda za ta yi wasanni shida har da daya a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League a bana.
A cikin watan Janairu aka fitar da Real Madrid daga gasar Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey na bana wanda hakan yasa yanzu gasar La liga da kofin zakarun turai ne kadai gasar data ragewa kungiyar da zata iya lashewa.
Saboda haka ya zama wajibi Real Madrid ta saka kwazo a watan na Fabrairu, idan ba haka ba ta fuskanci kakar bana ba tare da ta lashe kofi ba kuma Real Madrid za ta fafata da kungiyar Balladolid a wasan tan a gaba.
Sannan kwana uku tsakani Real Madrid za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Getafe a kwantan wasan tun na makon farko da basu buga ba sakamakon dage wasan da akayi saboda nisan da sukayi a gasar zakarun turai na kakar data gabata.
A dai makon wato ranar Lahadi Real Madrid za ta buga gasar La Liga a gida da kungiyar Balencia a filin ta na Di Stefano sannan daga nan ne Real Madrid za ta ziyarci Real Balladolid a gasar La Liga ranar Lahadi 21 ga watan na Fabrairu.
Real Madrid za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Atalanta domin buga wasan farko a zagaye na biyu a gasar Champions League ranar Laraba 24 ga wata sannan kungiyar za ta karkare watan Fabrairu da gasar La Liga da za ta karbi bakuncin Real Sociedad.