Connect with us

WASANNI

Watakila Henry Ya Zama Mataimakin Arteta A Arsenal

Published

on

Tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry yana daya daga cikin wadanda ake tunanin zasu zama mataimakan wanda ake tunanin zai zama mai koyar da yan wasan Arsenal, Mikel Arteta a karshen kaka.

Henry dai yanzu shine mataimakin mai koyar da tawagar yan wasan kasar Belgium inda kuma duka masu koyar da yan wasan kasar da mataimakansa sun amince zasu cigaba da zama domin cigaba da aikin koyar da yan wasan kasar banda Henry.

A na sa ran dai Mikel Arteta ne zai zama mai koyar da yan wasan Arsenal nan gaba kadan kuma tuni aka fara rade radin cewa zai dauki dan wasan kungiyar, Santi Carzola a matsayin mataimakinsa kuma dan wasa.

Sai dai har yanzu Henry bai tabbatar da aikin na Arsenal ba inda ya bayyana cewa bazai ajiye aikinsa ba na mai sharhi akan wasanni a kafar wasanni ta Sky Sports bayan dayace sai dai ya raba aikin biyu.

Henry dai zai cigaba da aiki da tawagar yan wasan kasar ta Belgium har sai bayan an kammala gasar cin kofin duniya kafin kuma ya bayyana inda zai koma inda ake tunanin Arsenal din dai zai koma.

Kasar Belgium dai zata buga gasar cin kofin duniya kuma tanada yan wasan da suka hada da Lukaku da Kebin De Bruyne da Hazard da Fellaini da sauransu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: