Ana tsammanin hadakar kwamitin majalisar dattijai da na majalisar wakilai za su amince da kasafin kudin shekarar 2021 a ranar 10 ga watan Disambar shekarar 2020. An bayar da rahoto cewa, har yanzu kwamitotin ba su mika rahoton ma’aikatu da rassa da cibiyoyin gwamnati ba. Sannan kuma majalisa ba za ta gudanar da sauraron jin ra’ayin mutane a kan kudaden sakamakon cutar Korona.
A ranar 20 ga watan Oktoba ce, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa, za a samu kammala komai kafin nan da zuwa ranar 3 ga watan Disamba. Amma a ranar 24 ga watan Nuwamba, Gbajabiamila ya koka ga yadda kashi 40 na kwamitocin ba su mika rahoto bag a majalisa.
A ranar 22 ga watan Oktoba, majalisa ta dage zamanta domin a samu damar gudanar da daftarin kasafin kudin shekara 2021 na ma’aikatu da rassa da cibiyoyi. An dai fara mika rahoton ne tun a ranar 18 ga watan Nuwamba.
Da ya ke zantawa ga manema labarai a ranar Litinin, mataimakin shugaban kwamitin majalisa mika rahoton, Iduma Igariwey ya ce, “an dai takatar da sauraron jin ra’ayin mutane ne sakamakon cutaar Korona, wannan shi ne babban dalili. Ba mu da isasshen waje da zai dauki mutanen da muka saba gayyata.
“Mun yi tsammanin za mu yi amfani da zauran majalisa, amma sai muka ga hakan ba abu ba ne mai yuwuwa a gudanar da sauraron jin ra’ayin mutane a wurin. Wannan shi ne babban dalilin da muka dakatar da sauraron jin ra’ayin mutane wannan shekarar.”
Da yake gudanar da jawabi a kan rahoton kasafin kudin, Igriwey ya bayayyana cewa, “ana bayyana cewa, kwamitoci da dama sun mika rahoton kasafin kudinsu ga kwamitin amsar rahoton kasafin kudin.
“Ina tunanin abin da ya fi dacewa shi ne, majalisa ta kammala dukkan ayyukan kasafin kudin da shugaban kasa ta aike mata kafin karshen wannan shekara kamar yadda kundin tsarin mulki ta tanada.
“Kwamitocin hadaka na majalisar dattijai da na wakilai na amsar rahoton za su kammala amsar dukkan wani rahoto a ranar 3 ga watan Disamba, yayin da majalisa za ta amince da kaafin kudin a ranar 10 ga watan Disamba,” in ji Igariwey.