Babu tabbas ko dan wasa Paul Pogba zai sake buga wa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wasa a kakar bana, a cewar kocin rikon kwarya na kungiyar Ralf Rangnick sakamakon raunin da ya ji. Kwantaragin dan wasan na tsakiyar Faransa mai shekara 29 zai kare a karshen kakar wasa ta bana, kuma ya fita daga wasan da Manchester United ta sha kashi a hannun Liberpool da ci 4-0 ne minti 10 kacal da fara wasan.
Ana sa ran dan wasan zai yi jinyar mako hudu akalla, yayin da United za ta buga wasanta na karshe ranar 22 ga watan Mayu da Crystal Palace kuma a cewar kociyan kungiyar abu ne mai wuya ya sake buga wasa har sai karshen kaka.
Da aka tambaye shi ko Pogba ya buga wa Manchester United wasan karshe, sai kocin ya amsa da cewa likitoci sun fada masa cewa Pogba zai shafe mako hudu akalla kafin ya warke kuma wasan da United za ta buga na karshe a karshen watan Mayu ne saboda haka babu tabbas idan zai sake buga wasa.
Pogba ya fara buga wa kungiyar matasa ta United wasa kafin daga baya ya koma Jubentus a shekarar 2012, sannan ya sake komawa United kan farashi mafi tsada a duniya a lokacin na fan miliyan 89 a shekarar 2016. A karo na biyu da ya koma kungiyar, dan wasan da ya lashe kofin duniya ya zura kwallo 39 cikin wasanni 226 da ya buga wa United, inda ya taimaka mata lashe League Cup da Europa League a 2017.