Connect with us

LABARAI

Watan Azumi: Gidauniyar Continental Ta Raba Miliyan Shida A Karamar Hukumar Rimi

Published

on

Gidauniyar Continental ta kara kafa tarihi inda ta raba kudin tsaba har sama da naira miliyan shida ga mutanen karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina domin saukaka hidimar watan Ramadan kamar yadda ta saba yi duk shekara.

Wannan Gidauniya na karkashin kulawar Dan Kasuwa mamalakin Kamfanin Continentan Computers, Alhaji Salisu Maman Kadandani, wanda ya yi suna wajan taimakawa al’umma ta bangare daban-daban.

A shekaranjiya Laraba An shirya taron rarraba kudade ga al’umomin karamar hukumar Rimi domin yin hidimar watan Azumi inda gidauniyar ta raba kayan azumi musamman irin wannan yanyin da ake ciki.

Da yake jawabi a wajan wannan rarraba, shugaban giduniyar, Alhaji Salisu Mamman ya bayyana cewa kafin wannan shirin dama, sun kaddamar da wani shiri na taimakawa al’umma inda za su ba mata dubu daya naira dubu goma-goma sannan kuma gidauniyar zata ba dalibai dari bakwai naira dubu goma-goma.

“Tuni mun kammala shirye-shiryen yin wancan biki amma saboda annobar Korana muka dakatar da wannan shiri, saboda haka da zaran abubuwa suka fara daidaita, to za mu hada taro kamar yadda muka yi wannan domin mika wannan gudunmawa ga wadannan dalibai da kuma mata na karamar hukumar Rimi.” Inji shi

Kamar yadda aka bayyana jadawalin raba wadannan kayayyaki wanda wannan gidauniya ta raba sun kasance kamar haka; Buhunnan gero 105 wanda kiyasin kudinsu ya kama naira miliyan daya da dubu dari biyu da bakwai da dari biyar.

Sannan akwai buhunan masara 105 wanda shima kudinsa suka kama miliyan daya da dubu dari biyu da bakwai da dari biyar, sai katan din taliya dari da biyar wanda kudinsu suka kama dubu dari uku da hamsin da bakwai.

Kazalika gidauniyar ta raba kudi naira miliyan daya da dubu dari hudu ga wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta karamar hukumar Rimi domin yin hidimar wannan watan da muke ciki.

Sai kuma sama da miliyan daya ga Limamai da uwanyen kasa masu rike da sarautar gargajiya na karamar hukumar Rimi, haka kuma an ware naira dubu talatin domin jigilar kayan zuwa mazabu goma da ke karamar hukumar Rimi.

Haka kuma an ba shugabannin jam’iyyar APC a matakan karamar hukuma da mazabu kudaden sayen sikari da gero wanda jimlar kudin baki daya shugaban wannan gidauniya ya bada tallafin sama da naira miliyan shida.

Taron dai ya samu halartar duk wani mai kishin karamar hukumar Rimi da suka hada da Babban Daraktan hukumar kula da gyaran hanyoyi ta jihar Katsina (KASROMA) Engr. Surajo Yazid Abukur da Hon Nasiru Ala Iyatawa da Hon Gambo Abdukadir Rimi da sauran uwayen kasa da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Rimi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: