Connect with us

LABARAI

Watan Azumi: Sanata Mandiya Ya Raba Miliyan 30 Ga Mutanen Shiyyar Funtua -Bala Abu

Published

on

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Funtua ta jihar Katsina Sanata Bello Mandiya ya bada naira miliyan talatin ga shuwagabannin jam’iyar APC na shiyyar dan gudanar da azumi cikin sukuni.
Mataimakin shugaban jam’iyar APC na shiyyar ta Funtua Bala Abu Musawa ya ya bayyana haka a lokacin da yake mika tallafin a madadin Danmajalisar ga shuwagabanin jam’iyyar
Alhaji Bala abu Musawa ya bayyana yadda suka raba kudaden inda yace an ba masu rike da shugabancin jam’iyyar a matakin gundumoni guda 177 naira N200,000 kowane sai shuwagabannin jam’iyya a matakin kananan hukumomi goma sha daya da ke shiyyar suma an basu naira N200,000 kowane.
Ya kuma ka ra da cewa suna shuwagabannin jam’iyar na jiha an basu 500,000 kowane domin dai a yi hidimar watan azumi cikin walwala da sukuni wannan kuma acewarsa daman an saba yi ba wannan bane karon farko
“Akwai masu ruwa da tsaki kamar, Limamai da Hakimai da shuwagabannin Mata da Matasa na jam’iyyar APC na yankin Funtua an basu naira N15,00 kowannensu.” Inji shi
Abu na biyu ya bayyana cewa su a karamar hukumar Musawa ‘yan gata ne a fannin siyasa, inda yace a da ana masu dariya cewar bana ba Sanata Abu Ibrahim an ga yadda za su kare, sai Allah ya kawo masu dauki wasu daga cikin yaransa suka zo suka ce sun hutar da Abu Ibrahim, daga cikin wadanda suka taimaka masu akwai Akawunta na jiha Malik Anas wanda ya basu buhun gero dari sikari buhu dari domin a tallafawa mutanen da ke gidan Bala a siyasa.
A jawabinsa Alh Bala Abu Musawa, yace badan Allah ya kaddari ‘bullar Annoba ta oronabirus ba, da yanzu Sanata ya fara gudanar da aiyukan ruwan sha a dukkanin kananan hukumomi sha daya na shiyyar Funtua,
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: