El-Zaharadeen Umar" />

Watan Azumi: Sanata Ya Raba Kayan Naira Miliyan 34 Ga Mutanen Mazabarsa

Sanata mai wakiltar Katsina ta kudu Sanata Abu Ibrahim ya raba kayan azumi ga mutanen mazabarsa na naira miliyan talatin da hudu da rabi domin saukaka rayuwa cikin watan azumi.

Da yake raraba kayan a madadin Sanatan mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Futuwa Bala Abubkar Musawa ya ce raba wadannan kayayyaki zai taimaka wajan saukaka radadin rayuwa a wannan lokaci na azumi.

Kayayyakin da Sanatan ya rarraba sun hada da buhunnan shinkafa da na suga da na gero kuma an raba su a kananan hukumomin goma sha daya da suke yankin Funtuwa inda yake wakilta

Bala Abubakar Musawa ya kara da cewa kowace karamar hukuma sun riga sun samu na su kason abinda kawai ya rage shi ne a cigaba da rabawa kamar yadda aka tsara ake yi kowace shekara, kuma ya yi kira garesu da su yi amfani da kayayyaki yadda ya kamata.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ya kara da cewa daga cikin wadanda za su amfana da wannan tallafi sun hada da limaman juma’a a kowace shelkwatar karamar hukumar a dukkanin kananan hukumomi sha daya.

Haka kuma ya yi kira ga mutanen yankin Funtuwa da su cigaba da yi wa gwamna Aminu Bello Masari da Sanata Abu Ibrahim addu’o’I domin samun nasara acikin harkokin mulkinsu tare da nuna goyan baya ga manufufinsu na alheri

Da yake nasa jawabin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi kira ga dukkanin wadanda aka zaba da su yi koyi da Sanata Abu Ibrahin wajan taimakawa masu karamin karfi a wannan watan na ramadhan mai albarka.

Gwamnan wanda mai taimakawa mashi na musamman akan ayyukan na musamman, Alhaji Shamsu Sule Funtuwa ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da su zama masu hadin kai musamman yanzu da zabe yana kara karatuwa.

Exit mobile version