Connect with us

FILIN FATAWA

Watanni Nawa Miji Zai Iya Kaurace Wa Matarsa Ta Sunna?

Published

on

Assalamu alaikum. Tambaya  ita ce, shin tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya kaurace wa matar shi ta Sunna kuma wani mataki ya dace ta dauka in har ya wuce period (wa’adin) da shari’a ta halatta 

Wa’alaykumussalam, Ya halatta ya kaurace mata tsawon watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a suratul Bakara aya ta: 226. Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da kansa ya cigaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin surar ta nuna hakan. In ya ki komawa ya sadu da ita kuma ya ki saki sai taje wurin Alkali don ya bashi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo mata ko kuma ya sake. Allah ne mafi Sani.

Yaushe Ake Yi Wa Yaro Kaciya A Mahangar Shari’a 

Assalamu Alaikum malam, ina tambaya ne a kan yiwa yaro kaciya, shekara nawa ya kamata a yi masa?

Wa’alaikumus salam, To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za’a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa: Babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da zata iya makalewa a al’aura. Wannan yasa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari’a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba’a yi masa kaciyar ba.

Daga cikin ka’aidojin malamai shine duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dankarami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7\ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa. Don neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349. Allah ne mafi sani

………………………

Ina Yawan Waya Da Budurwata, Ko Ya Halatta A Shari’ance?

Assalamu alaikum Dan Allah ina tambaya. Namiji ne yake so ya kara aure to shi ne bayan ya dawo gida da dare sai budurwar ta rika kiran shi ko kuma ta rika turo tedt (sakon waya), shi kuma idan matarshi tana kusa sai ya rika aboiding (kauce wa amsawa) amma da ta dan daga sai shi ma ya fara respinding (amsa wa budurwar) ko ya kira ta, kuma idan asuba ta yi sai ta kirashi. To shi ne matar ba ta so, dan Allah a Shari’ance yana da laifi ko ba shi da? Sannan matar za ta iya neman ya dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari’ance?

Wa alaikum assalam To dan’uwa yana da kyau ka san cewa matar da kake nema aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka dinga hira da ita ba, sai gwargwadon bukata. Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana daga cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya kirga jin dadin zancen wacce ba muharrama ba daga cikin ayyukan da Allah ya hana. Duk wanda yake yawan hira da matar da ba muharramarsa ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin dadin zancen matarsa ta halal. Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku, ku aikata katon sabo, yana daga cikin ka’idojin shari’a toshe duk hanyar da take kaiwa zuwa barna.

Zunubi shi ne abin da ya sosu a ranka kuma ka ji tsoron kar mutane su yi tsinkayo, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta: 2553. Allah ne mafi san  .

Idan Na Kusanci Mijina, Yana Kyamatata, Ina Mafita?

Assalamu alaikum Malam, ni ce ina da miji a duk lokacin da zan zo kusa da shi sai ya ce min barci yake ji, ai shari’a ta hana na dame shi, a haka za mu yi kusan wata ba abin da ya shiga tsakanina da shi, Allah taimaki Malam, mece ce mafita?

Wa’alaikum assalam, ki tambaye shi dalılin da yasa yake yin hakan, zai iya yiwuwa kin bata masa rai ko kuma akwai Wata matsalar, amma ta hanyar tambaya ko shigar magabata lamura za su iya fitowa fili. Shari’a ba ta halattawa namiji ya ki saduwa da matarsa ba da gangan, saboda nau’i ne na cutarwa, yana dağa cikin manufofin aure katange ma’aurata daga kallon haram. Allah ne mafi

Zan Saki Matata Saboda Tana Da Cutar Aids?

Assalamu alaikum. Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce bani da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara ?

Wa’alaikum assalamu To dan’uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, wadanda ba’a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, saidai  idan muka duba manufar da ta sa aka shar’anta saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma’aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai hadari kuma  ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin tun da malaman Fikhu sun halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil Sharhu Muktasarul Khalil: 6\478 Cutar Sida kuma tafi kuturta tsanani.

Sannan ba za’a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka’idojin Sharia: kau da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan yasa ba za’a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin. Allah ne mafi sani
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: