Abba Ibrahim Wada" />

Watford Ta Sayi Pape Gueye Daga Faransa

Kungiyar kwallon kafa ta Watford ta dauki mai buga wasan tsakiya Pape Gueye kan yarjejeniyar shekara biyar daga kungiyar da ke buga gasar Likue 2 Le Habre bayan wata doguwar tattaunawa da akayi tsakanin kungiyoyin biyu
Kwantiragin dan kwallon tawagar Faransan zai fara da Watford ranar 1 ga watan Yuli kamar yadda rahotanni suka tabbatar kuma da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa dan wasan zai fara daukar horo da kungiyar.
Yarjejeniyar dan wasan zai kare da Le Habre a karshen kakar wasa ta 2019 zuwa 2020, sai dai kuma gwamnatin Faransa ta soke gasar Likue 1 da 2 da duk wasu wasanni har sai zuwa watan Satumba mai zuwa.
Faransa na shirye-shiryen cire dokar hana fita a cikin watan Mayu, bayan da ta hana taron mutum 5,000 a waje daya saboda tsoron yada cutar korona kuma tuni aka fara sassauta wasu dokokin da aka kafa a kasar tun wajen watanni biyu baya.
Watford tana saman kungiyoyi uku da ke karshen teburin firimiya da tazarar kwallaye, ranar 7 ga watan Maris ta buga wasan karshe daga baya gwamnatin Burtania ta soke dukkan al’amuran wasanni sakamakon bullar annobar Korona.
Dan wasan zai kasance dan wasa na farko da wata kungiya ta saya a kasar Ingila a wannan kakar kuma tuni shugabannin kungiyar ta Watford sun kammala shirye shiryen gwada lafiyar dan wasan da zarar an bada damar yin zirga-zirga ta jirgi.
Pape Gueye dai ya buga wasanni da dama a kungiyar Le Habre, kungiyar da Manchester United ta sayo dan wasa Paul Pogba tun yana dan shekara 16 a duniya sai dai ana dab da tsayar da wasanni ya samu rauni amma yanzu ya warke

Exit mobile version