Connect with us

LABARAI

Watsi Da Mata A Siyasa Ya Sa Na Fito Takarar Kansila – Hajiya Rashida Ahmed

Published

on

Hajiya Rashida Ahmed wadda take neman takarar kansila a gundumar Gitata, Panda da Karu dake jihar Nasarawa ta bayyana cewa ba komai ne ya jawo ra’ayin ta ga tsayawa takara ba sai don yadda ake yawan barin mata a gefe a duk wasu harkokin da suka shafi siyasa. Wanda hakan ya sa matan ba su cika amfana da romon dimokradiyya ba.

Hajiya Rashida, wadda ita ce mace ta biyu da ta taba neman takarar kansila a wannan gunduma, ta kara da cewa ba ta jin dadin yadda maza ke jawo mata a jikin a yayin yakin neman zabe amma da zarar an cimma nasara sai a watsar da su a gefe ba za a sake waiwayar su ba sai wata kakar zaben.

“Dole ne a halin da muke ciki yanzu duk wani sha’ani a tafi da mata musamman a al’amuran siyasa saboda suna taka muhimmiyar rawa. Amma abin mamaki sau da yawa da an ci masara sai a bar su a baya. Ba tare da la’akarin cewa su ma suna fa gudummawar da za su iya bayarwa ba idan aka ba su mukami ko aka tsayar da su takara.

“Wannan shine dalilaina na fitowa takara domin ganin na kawo ci gaba a harkokin mata da matasa, domin duk shugabancin da za a kula da rayuwar mata da matasa, to za a samu nasara”, cewar Hajiya Rashida.

Game da ko me Hajiya Rashida ta taka har ta zama kallabi tsakanin rawuna, wato mace daya a cikin mazaje ‘yan takara, sai ta kara da cewa ba ta da kowa sai Allah shi zai dafa mata har ta kai ga nasara, sai kuma Ubangidanta, Alhaji Aliyu Musa Turaki (Tafidan Gurku) da ya tsaya mata da kuma mata da matasa da dama da suka nemi ta fito takarar domin share musu hawayen su. Haka kuma kungiyar su ta ‘Karu Women Debelopment Association’ su ma suna daga cikin wadanda suka mara mata baya domin tsayawa takarar.

Game da ko wane irin romon dimokradiyya mata ‘yan uwanta da matasa za su sharba idan har Allah ya ba ta nasara, Hajiya Rashida ta kara da cewa “ni yanzu ina da ‘yar sana’ata da nake gudanarwa a gida kuma Alhmadulillah ina samun rufin asiri.

“Don haka ina da burin ganin na karfafawa mata da matasa gwiwa wajen koya musu sana’o’i tare da ba su jari. Wanda ire-iren hakan muka rasa a wurin yawancin ‘yan siyasar da muke da su a yanzu”.

Hajiya Rashida ta kuma kalubalanci masu kallon mata ‘yan sisaya a matsayin karuwai ko marasa kamun kai, inda ta bayyana hakan a  matsayin kuskure domin siyasa a yanzu ba ta tafiya saida mata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: