Kwamared Sunusi Mailafiya" />

Wawaye Kan ‘Operation Amotekun’

Na sha faɗa cewar harkar tsaro a Nijeriya ta kai matsayin da take neman gagagar kundila, abin nufi shine, hakan yana neman gagarar Gwamnati taga karshen irin tutsun da ƴan kisan sari ka noke suke yiwa al’ummar Kasar nan, bawai ana magana iya arewacin Kasar bane da Boko haram ta gallaza musu, a’ah matsala ce data shafi Kasar gabadaya. Babu wani wanda yake musanta cewar tsaro a kasar nan ya taɓarɓare, matafiya basuda kwanciyar hankali har sai sunje inda zasu sun dawo gida tukunna. Dubunnan mutane da suke gudun shiga mota don biyo hanyar Kaduna daga Babban birnin tarayya, shima rahotanni sunce irin waɗannan masu satar mutanen sun afkawa wasu da harbi a tashar jirgin dake Kaduna. Banda kuma wanda ake bi ake musu ɗauki ɗaiɗai.

Gwamnonin Kudu maso yamma sun kirkiro shirin ‘Operation Amotekun domin su samar wa da yankunan su tsaro da kansu, duk da cewa yadda za’a tafiyar da shirin akwai ayar tambaya a cikin sa, domin zai iya zama hanyar da Gwamnati mai ci zata bi domin gallazawa ƴan jam’iyyar adawa, ire-iren waɗannan tsarukan sune kawai ya kamata yankin su gyarashi.

Tun da aka fara dambarwar wannan shiri na Amotekun mutane ke kirana domin suji matsayata akan hakan. Ni dai abu ɗaya nasani shine, wannan babban kalubale ne ga yankin arewa daya zama tamkar wata magudanar jinin al’umma, amma babu wanda yai tunanin kawo wani shiri don kare kai tunda hakan yana nema ya gagari jami’an tsaron. Kullum tunanina yana bani cewa daga kashe-kashen Boko haram zuwa irin kashe-kashen da aka dinga yi a jihohin Zamfara da Katsina, tabbas akwai wani kullallen abu da yake a ɓoye. Mu fadawa kanmu gaskiya, yankin arewa yankine mai matukar arziki, ƴan Boko da manyan ƴan siyasa. Yankine daya zama tamkar shine yake juya akalar tafiyar Kasar, amma kuma babban abin bakinciki shine yadda mutanen yankin ke shakulatin bangaro da al’amuran yankin. Yadda Kudancin Kasar nan ke kishin yankin su, ƴan arewa basayi. Yadda ƴan Kudancin Kasar nan daya hada da Inyamurai da Yarabawa ke tsayawa mutanen su, arewa basayi, sai kishi a baki, amma a fili, babu komai sai hassada, kyashi da kuma son rai, wannan itace ta janyo duk wata shara idan aka ɗauko zakaga a yankin arewa ake ajjiyeta. Wani Dakta ya taɓa gayamin cewar jihohin kudu nawa na sani da cutar sauro (malaria) ta takurawa, nace gaskiya banda lissafi. Sai yacemin to Gwamnati idan taga damar kawar da wannan cutar, tabbas zata kawar da ita, amma kuma an cusheta a arewacin mu, ance mune mukeda sauraye, duk wata allurar rigakafi da me amfani da mara amfani sai akawo mana. Haka idan ka ɗauki harkokin noma, shin wane yankine yafimu noma, amma shin muna amfana da noman? Shin manyan Attajirai nawa muke dasu a yankin na arewa, amma shin wane huɓɓasa sukayi a harkokin noma, da yawan su kamfanonin su a can Kudancin suka ginasu, na farko jihar ta samu haraji, sannan an samarwa ƴan jihar aiki, banda kuma tallar sunan jihar da akayi a duniya.

Yau Boko haram ta zame mana alakakai, ta uzzurawa kowa, sun gagari Gwamnati ballantana farar hula su iya kare kansu. Yau shekara nawa da ɓullar su, amma wane karfin gwuiwa muke dashi cewar anci karfin su. Abin bakinciki ko a Gwamnatin baya, wanda aka bawa kuɗin makaman da za’a siyo domin yaki da waɗannan mutane, ɗan arewa ne, amma muna gani yayi bandar kuɗin hankalinsa kwance, saboda babu wani nasa da aka taɓa kashewa, shin wannan ba abin kunya bane?

Shugaba Buhari yayi matukar mamaki cewar har yanzu akwai Boko haram. Sam kalaman sa ba abin mamaki bane, sai ma tsoratarwa a garemu. Idan har Shugaban samar da tsaro kuma babban kwamandan askarawan Kasar baisan halin da tsaron Kasar yake ciki ba, to wanene zaisan halin da ake ciki? Ina cewa sai masu iko sun san halin da ake ciki, sannan za’a san wane irin mataki za’a ɗauka, shin anci galaba akansu ne, ko kuma a’ah sunanan suna kisan al’umma, sannan asan wasu hanyoyin da za’a kuma ɓullowa dasu.

A yau rahotanni da dama na nuna cewa Nijeriya tana ɗaya daga cikin jerin kasashen da suke da hatsari saboda rashin tsaro. Babu wani wanda yake da tabbas ɗin tsaron lafiyar sa. A layin ku za’a iya samun ɓatagari su tareka, su bubbugeka kuma su kwace duk abu me daraja a hannun ka, idan ma katafi caji ofishin ƴan doka, me zasu iyayi? Zaka cike abinda ya faru ne kawai domin hakan akeyi, amma kai kanka ba kada karfin gwuiwar cewa za’a kama waɗannan mutane. Haka yake faruwa idan barayi sun haurawa mutum gida, suyi abinda suka ga dama, amma babu maganar bincike ya samo su, ballantana kuma waɗanda ake garkuwa dasu, kyakkyawar shawarar da za’a bawa iyalan wanda aka rike shine, ace kuyi ciniki yadda zaku iya fansar ahalinku kawai, wannan wace iriyar kasa ce?

 

Exit mobile version