DAGA SAMEERAH BELLO SHINKO,
,A wannan zamani da muke, idan ka duba a cikin al’ummar mu, waya ta zama ruwan dare a tsakanin kananan yara, matasa, mata, maza kai har da dattijai ma. Ganin hakan ne ya sa na yi bincike a kan amfanin waya ga mata da kuma irin illar amfani da ita.
SHIN MENENE WAYAR SALULA?
Da zarar an ambaci kalamar wayar salula abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne; wata na’urar zamani mai saukaka isar da sako. Ko dai ta hanyar sakon karta- kwana, ko kiran gaggawa a fadi wani abu da a baya sai an dauki tsawon lokaci kafin sakon ya isa in da ake bukata.
Wasu kuma za su iya kallon wayar salula a matsayin Jakadiyar sada zumunci, ko kuma ‘yar aiken da ke isar da sako da wuri; har ta ceto rayuwar wani ko wasu mutane daga fadawa wani masifar. Misali fashi da makami, gobara, hadarin mota, rashin lafiya, kwantar da tarzoma, isar da sakon farin ciki ko akasin haka.
Wayar salula na taka muhimmiyar rawa a rayuwar mata ta yau da kullum. Sai dai kuma ta kan taka rawa wajen haddasa fitina ko gurbata tarbiyya, da haddasa rashin jituwa tsakanin miji da mata ko kawaye har ma da gurbata tarbiyyar ‘ya’yanmu.Kafin mu san illolin ta, ga wasu daga cikin amfaninta gare mu:
AMAFANIN WAYAR SALULA GA MATA
- Zumunci: kamar yanda aka sani, dama mata sune iyayen zumunci. Samuwar waya ta taimaka musu sosai wurin kara sada zumunci, ta hanyar hada ‘yan’uwa wanda suke nesa da juna.
- Kasuwanci: Waya ta taimaka sosai wurin hana mata zaman banza, har da irin wadanda mazan su basa son suna aikin gwamnati. Saboda ta zo da hanyoyin gudanar da harkokin kasuwanci daban-daban, mace tana cikin gidan ta. A yau daga gida mace za ta iya dora sana’ar ta ko haja, mutane su gani su saya ta aika musu ba tare da ta bar gidan mijin ta ba.
- Agajin gaggawa: Wayar Sailula ta taka muhimmiyar rawa wurin sadarda agaji na gaugawa. Misalin mace za ta iya kiran mijinta idan bata da lafiya ko yaranta,shi kuma baya gida ko ya yi tafiya. Daga can din kuma ya turo a bata taimakon gaggawa.
- Mata na amfani da waya wurin Karin ilimi,ta hanyar shiga shafukan sada zumunta ko karance-karancen littafai ko ziyarar yanar gizo-gizo.
- Waya tana taimakawa mata wurin koyon sabbin girke-girke da kuma hanyoyin kula da miji duk a shafukan sada zumunta.
- Waya tana debewa mata kewa a lokacin da mazan su basa tare da su, idan sun yi balaguro.
- Haka zalika waya tana kara dankon kauna da soyyaya tsakanin miji da mata, kuma ta taimaka wurin rage yawan zuwa zance da samari ke yi gurin ‘yan matan su.
To wannan kadan kenan daga cikin alfanu na wayar salula ga ‘yan uwa mata. A binciken da na gudanar kuma, wanan sune kadan daga cikin illolin wayar salula ga mata:
- Sirri: A wannan zamani da muke ciki yanzu, zamani ne wanda sirri ya yi karanci. Zuwan wayar salula ya kara bata komai,in da za ka ga mata suna tona sirrin mazan su,kansu da gidaje su da sunan neman shawara,a shafuka na sada zumunta.
- Haduwa da kawaye bata gari: da yawa wasu matan tarbiyarsu na lallacewa ta hanyar haduwa da kawayen da ke basu shawara ko dora su a kan wata hanya da bata dace ba, misali shaye-shaye, neman mata ‘yan uwansu,daukowa miji rigima ta hanyar cin bashi, koma a ki zama lafiyar da miji kwata kwata. Idan ‘yan matane har sata da bin maza.
- Tabarbarewar karatu: da yawa yara mata karatun su ya lalacewa saboda waya,saboda hankalinsu ya karkata zuwa ga chatting,sauren wakoki ko kuma karatun littafan hausa.
- Lalacewar tarbiyya: Saboda samun ci gaba na zamani da ya auku, kamar yadda aka ambata a baya, wayar salula ta yi jagora sosai da gaske wurin wargaza tarbiyyar yara mata.Misali akwai abunda ake kira da ‘cybersed’ a Turance, ma’ana shi ne zina ta yanar gizo ko shafukan sada zumunta wanda hakan yana faruwa ba tare da sanin iyaye ba. Yana faruwa ta hanyar kiran waya ko kuma zance a shafukan sada zumunta. Masu wannan dabi’a suna bin hanyar taba al’aurar su dan su biyawa kansu bukata, da haka ake fara bata yarinya har ta fara aikatawa zahirance.
- Bata aure ko dangantaka tsakanin mace da mai neman auren ta:Ana haduwa da maza iri-iri a ‘social media’, idan aka yi rashin dace aka hadu da wadanda basu da imani, da haka za su mu’amilanci mace har su saka ta wata hanya da bata dace ba. Wasu ba ruwan su har matan aure bibiya suke,kuma a yanda mace take da rauni sai wacce ta yi taka-tsantsan kuma Allah ya tsare ta; idan ba haka ba hakan zai zamo sanadin rushewar aurenta. Da yawa wasu matan saboda matsalar da suke samu a gidan aurensu irin wannan mazan suna basu kulawa da soyayya har su karkata kansu su fada soyayyarsu. Daga haka sai su aikata mugun nufin su.
- Rashin Isasshen Barci: Hakika barci yana da matukar amfani ga jikin dan Adam. Amma da yawa zaka samu wasu mata sun kasha dare suna chatting ko karatun littafan hausa.
- Wasu matan basu bawa yaransu da mazan su kulawa saboda waya, ko dai karatun littafai ko tana can tana chatting, wani lokaci har a bar abinci ya kone.
- Bata lokaci:Waya tana bata musu lokaci sosai da wasu matan ma ibada tana musu wahala.
Mata dai su na bada dalilai daban-daban da ya sa suke amfani da wayar salula.Koma dai meye ya kamata ayi nazari mai zurfin gaske tsakanin amfaninta da kuma illolinta kafin rike wannan na’ura. Mace tayi amfani da kaifin tunani ta kuma yin taka-tsantsan idan rike wayar ya zama dole. Haka zalika, iyaye da mazan aure ya kamata su dinga kula da abinda ‘ya’yansu ko matansu suke yi,su na saka su a hanya. Allah yasa mu dace.