Idris Aliyu Daudawa" />

Wayar Da Jama’a Ne Mafita Kan Matsalolin Kiwon Lafiya – Likita

Dokta Fidelis Ekemba Likita ne wanda kuma ya bayyana cewar babbar hanyar za abi wajen fita daga matsalolin da suka shafi kiwon lafiyar al’umma a Nijeriya ita ce, wayar da kan al’umma. Idan aka yi haka din kamar yadda ya ce zai inganta lafiyar al’ummar Nijeriya matuka.

Dokta Fidelis Ekemba, wanda aka fi sani da suna: ‘Aproko’ Doctor, ya bayyana cewar ita harkar  wayar da kan jama’a da samun bayanan da suka dace su ne abubuwa wadanda zasu taimaka matuka wajen inganta al’amuran kiwon lafiyar kasar Nijeriya.
Ekemba ya bayyana wa Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Legas ranar Talata ta makon daya gabata cewar, har yanzu ana bukatar abubuwa masu yawa idan aka zo al’amarin kiwon lafiya a Nijeriya.
Ya cigaba da bayanin cewar “Yayin da ake samun nasara a wasu yankuna da kuma kananan yankuna; gaba daya, yanayin tsarin kiwon lafiyar kasa yana cikin talauci.
“Har yanzu ana daukar Nijeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da ke da babbar matsala a tsarin kula da lafiyar al’umma, kuma wani sashi na dalilin shi ne saboda irin nauyin da mutane ke da shi kan tsarin kiwon lafiya da ya rataya a wuyansu.  Likitan wanda  shine ya kirkiro @DHealthyThreads, ya  bayyana cewar Nijeriya tana da likita daya wanda yake kulawa da da fiye da mutane 10,000. Ya ce, kididdigar ta hadu da shawarar Hukumar afiya ta duniya na likita ɗ-daya zuwa tsakanin mutane 400 zuwa mutane 600 abinda ya dace ya kasance ke nan.
“Idan aka bayar da irin wannan bambancin a tsarin kula da lafiyarmu, har yanzu akwai sauran ayyuka da za a yi. “Don haka, wannan shine inda wayar da kan jama’a yakamata ya shigo ko kuma a shigo da shi.”
Ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya su hana jama’a zuwa asibitoci ba akan ka’ida ba. Ya ce yakamata su maida asibitin wurin da ya kamata mutane su je kawai lokacin da suke matukar bukatar yin hakan. kwararren likitocin ya bayyana cewar ta hakan ne za su rage nauyi a kan tsarin kiwon lafiyar kasar Nijeriya.
Ya kara jaddada cewar hakan zai ba ma bangaren  damar inganta  ayyukanta kiwon lafiya na al’umma.
Mutane suna bukatar sanin yadda ake yin rayuwa mai kyau. Yakamata su san lokacin da abubuwa suke tafiya ba daidai ba a jikinsu ko kuma tsakanin wadancan mutanen da ke kewaye da su.
“Mutane suna bukatar samun bayanan da suka dace don shawo kan su matsalolin. Bugu da kari kuma suna buƙatar sanin mahimmancin binciken likita, yadda ake tsabtace muhallinsu, tare da sanin alamun yadda ake kamuwa da wasu cututtuka da dai sauran su.”
Ya ce an dauki  likita aiki ne domin jama’a su san abin da ya kamata su sani kuma su yi dangane da yanayin lafiyar su.
Ya kara bayar da haske cewar hakan ne ma yakamata su sami damar cike gibin rashin sani da matsalolin da suka mamaye muhallinsu.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa ni da wasu likitocin  muka yi kokarin inganta wayar da kan ‘yan Nijeriya na yau da kullun saboda yin hakan zai taimaka wajen inganta harkar lafiyar  a Nijeriya.
‘Aproko’ a zahiri yana nufin mutumin da ke yin hayaniya mai yawa, wani wanda yake leken asiri ko kuma bai damu da wani abinda yake na shi ba.
“Kuma mun lura da cewa hanya mafi kyau da za a jawo hankalin ‘yan Nijeriya ita ce ta amfani da kafafen sada zumunta; saboda matsakaicin mutum yana amfani da kimanin sa’o’i hudu a cikin kullun a kan kafofin watsa labarun kadai.
“Don haka, na ce me zai sa ba za ku je can ku gwada yadda zan iya yin tasiri ga ‘yan Nijeriya gaba daya ba kuma inganta tsarin kula da lafiyarsu, yayin da kuma a lokaci daya na taimaka masu wajen inganta al’amuran lafiya na Nijeriya.”
Ya  kara bayanin cewar an dauki sunan ‘Aproko’ Doctor saboda ya jawo hankalin mutane masu yawa wadanda daga baya suka yarda da shi. Ya ce sakamakon da ya samu ya nuna cewa likitan ‘Aproko’ bai yi mummunar barna ba.
“Wannan shekara ta biyu ke nan da kasancewarta. ‘Ina ganin mun yi kyakkyawan aiki. Ina tsammanin shaidu daga mutane sun kasance: Ina cin abinci mafi kyau saboda Aproko Doctor. “Ina yin abubuwa da yawa fiye da yadda nake yi a baya.”
Ya ce hanyarsa ta gaba ita ce cewa ya yi niyyar yin aiki tare da hukumomin kasa da kasa tare da kai wa ga mutanen da ba su iya ba, kuma suna bukatar aiyukan lafiyarsa. “Kamar yadda muka samu damar mutane da yawa a shafukan sada zumunta, har yanzu akwai sauran da ba su da damar yin amfani da su.”
Wannan shi ne mataki na gaba, wancan shi ne inda mu ke son kaiwa yanzu kamar dai yadda ya bayyana.
Daga karshe ya ce a shirye ya ke ya bayar da hadin kai ga hukumomin kasa da kasa, masu saka jari da kuma mutanen da suke da sha’awar inganta yanayin lafiyar ‘yan Nijeriya.

Exit mobile version