Wayar Da Kai: Ma’aikatar Harkokin Mata Ta Shirya Gangamin A Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Kimanin mata da raya ƙ anana 150 ne suka amfana da shirin gangami da wayar kai akan sha’anin kula da tsaftar iyali da kuma sanin yadda za su dogara da kansu da muhali tare da lalubu hanyar da za su ƙ ara kula da inganta rayuwar yaransu domin kaucewa kamuwada cutar tamowa.

Ma’aikatar harkokin mata ta jihar Katsina ta shirya taron a garin Bani’iza da ke ƙ aramar hukumar  Ɓatagarawa a jihar Katsina.

Taron wanda aka gabatar da lakcuci daga masana daban-daban ya fi maida hankali akan sha’anin kula da lafiyar yara ƙ anana waɗanda suke fuskanci kamuwa da ciwon tamowa tare da jan hankali ga iyaye mata da su bada gudunmawa akan makarantar ‘ya ‘yansu mata.

A jawabinsa gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari  ya ce,  gwamnati ta ɗauki sha’anin kiwon lafiya da mahimmanci so sai, shi yasa take bada duk wata gudunmawa idan buƙ atar hakan ta ta so

Gwamnan wanda mai baiwa gwamna shawara akan harkokin zuba jari, Alhaji Ibrahim Tukur Jikamshi ya wakilta ya bayyana cewawannan shirin ya samu asali ne ta yin la’akari da kungiyoyin mata da aka kafa domin ilimintar da harkokin ilimin sanin addininsu kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada.

Ya ƙ ara da cewa a ƙ arƙ ashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ta faɗaɗa wannan tunina da ƙ oƙ ari na mata ta hanyar saka ilimin manya (Yaki Da Jahilci) da koyar da sana’o’I tare da wayar da kan mata ingantatun hanyoyin kiwon lafiya da kuma sanin inda gwamnati ta sa gaba.

Dakta Badiya Hassan Mashi ita ce kwamishiniyar harkokin mata a jihar Katsina ta yi ƙ arin haske dangane da wannan shiri na ganganmin wayar da kan iyaye mata, inda ta ce fiye da mutun ɗari da hamsi ne suka amfana da wannan shiri.

Sannan ta bayyana cewa taro ne na gamgami domin kulawa da mata da yadda za su koyi dogaru da kai na sana’a da ilimi da sauran abubuwa da suka danganci rayuwarsu ta yau da kullin.

Ta ƙ ara da cewa kowace maza ɓ a da ke faɗin jihar Katsina za a yi irin wannan taro kuma za a tabbatar an kula da  ɓ angaran kiwon lafiya a lokacin wannan gangami da zamantakewa da sauran harkokin rayuwa baki ɗaya.

Dakta Badiya Hassan Mashi ta bayyana cewa ya zuwa yanzu sun tantace mata da ƙ ananan yara150 inda suka kasa su kashi uku na farko an gwada su ba su da matsala ta tamowa kashi na biyu kuma sun nuna alamun kamuwa da ciwon tamowa sai kuma kashi na uku su 18 kuma tuni aka ɗauki mataki inda aka miƙ a su zawa asibiti domin yi masu magani

Daga ƙ arshen taron an raba wani sinadari da ake kira da garin lafiya wanda zai taimakawa ƙ ananan yara domin su ƙ ara samu kumari tare da inganta lafiyarsu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutar tamowa.Ta kuma ja kunnensu da su tabbatar sun yi amfani da garin lafiyar kamar yadda aka umarce su.

Exit mobile version