Abubakar Abba" />

Wayar Huawei Ta Zarce Apple Kasuwa

Wayar tafi da gidanka da ake kerawa a kasar China a yankin Huawei ta zarce wayar tafi da gidanka ta ta samfarin Apple duk da dakatar da ita da akayi a kasuwar kasar Amurka , inda ake ganin zata cike gurbin wayar tafi da gidanka samfarin Samsung ganin cewar, itace ke akan gaba a duniya. Banban jami’I na sashen hudda na Huawei  Richard Yu ne ya sanar da hakan  a cikin jawabinsa a lokacin da aka fitar da sakamakon kasuwanci na farkon shakarar  2018, inda kamfanin na  Huawei yace, zai fitar da samada wayoyin  smartphones miliyan 95, inda Haldane ya nuna an samu karin kimanin kashi  30 bisa dari. Ba wata abar tambaya bace na cewar zamu zamo na  biyu a shekara mai zuwa haka kuma a cikin tsakiyar shekara mai zuwa, zamu iya zamowa na daya kuma a cikin watanni shida da suka wuce lamarin ya kasance mai wuyar sha’ani. Richard Yu yaci gaba da cewa, Huawei ta zamo ta biyu akan Apple wajen kara yin matsi a cikin kasuwar  smartphone market a zagayen shekara ta biyu. Samsung a Kudancin kasar  Korea, tana a sama a cikin watan

Afrilu zuwa Yuni, inda ta fitar da wayoyin da suka kai yawan miliyan  71.5 da adadin ya kai kashi 20.9 a cikin kasuwa. Sai dai, Huawei ta sayar da wayoyi da suka kai miliyan 54.2, inda hakan ke nuna cewar, sun kai kashi  15.8 bisa dari a kasuwa,  inda  Apple kebi mata da miliyan  41.3 hakan kuma ya nuna tanada kashi 12.1 bisa dari a kasuwa. Har ila yau, wannan shine karo na faro tun a 2010 da Apple bata kai matsayin wadda suke a sama ba. Acewar IDC, miliyan  342 na  smartphones an shigo dasu a zagayen shekarar faro , inda hakan ya kai kashi 1.8 bisa dari duk a cikin lokacin na   2017 da kuma a cikin zagayen ahekara ta uku. Har ila yau, yanayin kasuwa da saukar farashi suna daya daga cikin abinda ya haifar da hakan. Wayar ta kuma samu karbuwa a nahiyar turai da nahiyar Afirka da kuma yankin Asiya. Acewar Mo Jia, wani mai fashin baki dake yankin Shanghai cin nasarar da ake nema kafin karshen  2019 tana cike da kalubale.

 

 

 

 

Exit mobile version