Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Waye Gwani Tsakanin Anthony Joshua Da Tyson Fury?

by Abba Ibrahim Wada
December 31, 2020
in WASANNI
3 min read
Anthony Joshua Da Tyson Fury
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kusan a yanzu za a iya cewa babu wani wasa da fagen Dambe da ake jira a ga yadda za ta kaya face wasa tsakanin matashi kuma shahararre wanda tauraruwarsa take haskawa a yanzu, Anthony Joshua da abokin karawarsa, Tyson Fury, dukkansu ‘yan kasar Birtaniya.

A sabuwar shekara mai kamawa ne ake tunanin gwarazan biyu zasu kece raini domin samun wanda zai zama babban zakaran duniya ta hanyar lashe kyaututtukan da a doka ake bukata domin samun wannan kambu.

samndaads

A kwanakin baya zakaran Anthony Joshua, ya bayyana cewa  ya gama shiryawa domin fafata wasa da Tyson Fury, dan burtaniya, a wasan da zakarun biyu zasu kece a sabuwar shekara mai zuwa domin fitar da zakaran da duniya zatayi alfahari dashi a gaba.

Kalaman na Joshua suna zuwa ne kwanaki kadan bayan shima Tyson Fury ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fafata wasan Dambe da zakaran wannan lokacin Anthony Joshua a wasan da ake saran za’a fafata a shekara mai zuwa a birnin Landan din Ingila.

Dukkansu gwaraza ne wadanda kuma kuma duniya take fatan ganin yadda zasu gwabza domin fitar da gwani wanda hakan zai faru ne nan gaba kadan musamman idan aka sake samun raguwar kamuwa da cutar Korona a Ingila.

A tsakiyar wannan watan  ne dan damben Burtaniya Anthony Joshua ya doke Kubrat Puleb, dan asalin kasar Bulgeria wanda hakan ya kara fitowa da batun karawarsa da Tyson Fury fili kuma Joshua ya yi nasara ne a fafatawar da aka kai zagaye uku ana yi.

‘Yan kallo 1,000 ne dai aka bai wa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bayar da tazara saboda annobar korona kuma jim kadan bayan nasarar da Anthony Joshua ya samu ne magoya bayansa suka rika fadar cewa ‘saura Fury’.

Furta hakan ke da wahala kuwa sai Anthony Joshua ya ba su amsar cewa ‘duk wanda ke da tarin kofuna ya zo na shirya’ kuma idan ma Tyson Fury ne, to shi ke nan a shirye yake ya kara da Tyson Fury’.

Ba da wata wata ba kuwa sai shima Tyson Fury ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ‘to kun ji amsar Anthony Joshua game da karawa da ni kuma nima na shirya, na matsu na doke shi’ cikin zagaye uku kacal”.

‘Yan kallo 1,000 ne aka baiwa damar shiga filin wasa na Wembley Arena, la’akari da daukar matakan bada tazara saboda annobar Korona sai dain idan ba’a manta ba kadan ya rage ganiyar Joshua ta ruguje a watan Disambar bara, a lokacin da ya dauki fansa kan Andy Ruiz Jr.

Kuma kisan da ya yi wa Kubrat Puleb a daren Asabar ya nuna cewa a yanzu Tyson Fury ne kawai ya rage su saka zare, don ya tabbatar wa duniya kololuwar inda kwarewarsa ta kai a duniyar dambe.

Tuni Joshua ya fara shafar rayuwar samari da yawa musamman a kudu maso yammacin Najeriya, kamar Legas babban birnin kasuwancin kasar domin da yawa daga cikinsu sun kalli yadda ya zama shahararre ya cika burinsa na rayuwa, kuma labarinsa kusan yazo dai-dai da nasu, na wanda ya sha wahalar rayuwa kafin daga bisani kofar arzikinsa ta bude ya sha kwana.

Labarinsa, wani abu ne da aka jima ana nuna irinsa a fina-finai irin na Nollywood, kamar dai ace na mutumin da burinsa na rayuwa ya cika bayan shan kwarba shekara da shekaru sannan Joshua ya zama wata sila ta samun karbuwar harkar dambe a Najeriya, domin a yanzu, har ta kai ga ana horar da mutane wasan a makarantu bayan tashi daga karatu, da kuma ranakun hutu da sauran wurare da dama.

Duk da cewa tsarin da ake da shi na yin harkar ba wani na azo a gani bane, amma duk da haka kwarin guiwa na zaburar da matasa da dama sakamakon hakan nan gaba za’a iya samun ‘yan dambe masu yawa a kasar nan domin akwai matasa da dama irinsu Lekem duka suna sha’awar wasan.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tun Ina Makarantar Firamare Na Ke Da Sha’awar Rubutu – Marubuciya Nafisat Aliyu

Next Post

Matsayin Neymar Da Mbappe A PSG

RelatedPosts

Pochettino

Pochettino Ya Kamu Da Cutar Korona

by Abba Ibrahim Wada
1 hour ago
0

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain Mauricio Pochettino ya...

Solkjaer

Ban Damu Da Jita-Jitar Korata Daga Manchester United Ba, Cewar Solkjaer

by Abba Ibrahim Wada
1 hour ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer...

ozil

Dole A Yiwa Ozil Hakuri – Zidane

by Abba Ibrahim Wada
1 hour ago
0

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real...

Next Post
Neymar Da Mbappe

Matsayin Neymar Da Mbappe A PSG

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version