A makon da ya gabata ne kungiyar SSANU ta kasa reshen jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta kira wani taron kara wa juna sani ga ‘ya’yan kungiyar karkashin Kwamared I.A Bello wanda ya bar baya da kura.
Taron ya samu karbu wa daga ‘ya’yan kungiyar da kuma manya daga cikin jama’ar kamar irin su D.B.C Adamic wanda an gabatar da kasida da za ta kara wa ‘ya’yan kungiyar kwarin gwiwa ta bangarori da dama.
Daga karshe ne Kwamared I.A Bello ya kalubalanci shugabancin kungiyar ta kasa da cewa ba su iya shugabanci ba illa shirme kamar yadda ya bayyana wa manema labarai a sakatariyar su ta SSANU da ke harabar jami’ar.
Haka ya sa wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kwamared Shu’aibu Khalil a kan ko me ya yi zafi a kan shugabancin kungiyar SSANU ta kasa da kuma kungiyar SSANU ta reshen ABU Zariya?
Sai Kwamared Shu’aibu Khalil ya kada baki ya ce, “Babu wanda ya san wani Kwamared I.A Bello a kungiyar SSANU ta kasa, mu abin da muka sani shi korarren shugaba ne bisa abin da ya faru a tsakaninsa da shugabannin kungiyar ta kasa. Shi ba mamba ba ne gaba daya, kuma dalilin shi ne bangaren zartarwar SSANU ta kasa ta dakatar dashi, kamar yadda wasikar mai kwanan wata 16/2/2018 ta bayyana ma dukkan ‘ya’yan kungiyar a kasa baki daya.
Wakilinmu ya nemi jin ko waye ya sa hannu a cikin wasikar dakatar da Leander I A Bellon?
Sai kwamared Shu’aibu ya ce, sakataren kungiyar SSANU na kasa ya sa hannu a wasikar, Kuma ya kara masa tambayar a kan ko an sanar da shi I A Bello dangane da matakan da shugabancin kungiyar ta kasa ta dauka a kansa? Kwamared ya kada baki yace, an sanar da shi, tabbas, kuma kwafin wasikar an kawo min sannan kuma anba hukumar gudanarwar jami’ar kuma ma anba shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Zariya yana da kwafi, rijistira ma yana da kwafi, dan haka an kore shi. Kuma kafin a kori Kwamared I.A Bello, an dakatar da Bello a ranar 28/5/2016 a wajen taron zartarwa ta kasa da aka yi a Michael Amadu Center of Labour Studies a jihar Kwara, an dakatar da shi daga baya ne ya tafi kotu domin daukar mataki kuma kotun ba ta tsayar da matakin da aka riga aka dauka ba, dan haka ne ma ya sa a ranar 23/1/2018 aka yanke shari’a ta karshe a kan wannan fayal da ya shigar da harkokinsukara a Kano, Alkali E.D.E Esele ya yanke hukunci, wato babban alkalin kotun National Industrial Kano, kuma alkalin ya yanke hukunci inda ya kori karar, inda ya bayyana shari’ar da bata lokaci ce kuma wani atisayen masana ne kawai, dan haka daga farko an dakatar da Bello, ya tafi kotu, kotu ta yanke hukunci kuma hukuncin na korar karar da ya shigar ne wannan na nufin ba wata gajiya, ko taimako ko biyan diyya a kan abinda ya kai karar babbar kungiyar kasa a kai, daga baya kuma sai aka kore shi kamar yadda kundin tsarin kungiyar ya tanadar, kamar yadda na gayamaka ta hanyar wasika mai kwanan wata 16/2/2018. To idan aka kori mamba, har yanzu yana cikin mambobin kungiya? Tabbas a’a, shi ba mamban SSANU bane kwata-kwata, to kuma saboda shi ba mamban SSANU bane ba ya da zarafi a cikin doka ya rika bayyana kansa a matsayin mamban SSANU, ba ma ya ce shine shugaba ba, Bello ba mamba bane a kungiyar SSANU.
Wani abin mama ki shi ne, kuma Kwamared I A Bello yana yin aikace-aikace daban daban na SSANU a jami’ar Ahmadu Bello Zariya da suka hada da taron karawa juna sani, taro da manema labaru da sauransu me ya sa kake tunanin hakan na faruwa yana ta yin wadannan ayyuka amma kana cewa shi ba mamba bane?
Sai Kwamared Shu’aibu Yace, yana yin wadannan ayyuka ne saboda goyon bayan da yake samu daga hukumar gudanarwa ta jami’ar Ahmadu Bello, tana bayyana ne hukumar gudanarwar jami’ar Ahmadu Bello kamar ta dauki bangare ne a matsalar.
Wakilinmu ya ce, me kake nufi?
sai kwamared ya ce, saboda hakkin hukumar gudanarwar jami’ar Ahmadu Bello ne ya yarda da a gudanar da taro a wani waje a jami’ar, misali idan Mamman Kwantagora Skuare , Assembly Hall an yarda a gareshi da ya yi taro wannan na nunawa karara a fili ga kowa ba ma sai mun yi tambayoyi ba cewa jami’ar tana goyon bayan gudanar da tarurrukan da ba kan doka suke ba a jami’ar, kuma ba ma wannan kawai ba, an kyale Bello ya ci gaba da zama a cikin sakatariyar da jami’ar ta gina wanda aka tanada domin wadanda suke a bangaren zartarwar SSANU, kuma kyale shi ya ci gaba da zama a wannan matsayi mai muhimmanci na nufin jami’ar tana goyon bayan hakan kuma wannan ne ya sa ya ke yin abinda ya ke yi. Idan da jami’ar ba ta goyon bayansa ba zai taba samun wata dama ya samu dakunan taro ya yi wani taro da ba kan doka ya ke ba. Kuma yana yin wannan tarurruka ne domin ya fito da wasu abubuwa daban, misali a taron farko da ya yi bayan dakatar da shi ya zo wata irin matsaya wadda ba ta gaskiya ba mai rudarwa, misali ya fito da matsaya cewa mayar da Chekue of due zuwa kungiya ta kasa hukumar gudanarwa ta tsayar da shi, kuma abin mamaki matuka shugaban jami’a ya karbi wannan wasika ya yarda ya aika wa Bursar domin a tabbatar, kuma tun wannan lokacin kungiyar kasa bata karbar cikakkun Chekue of dues wannan kuwa karya dokar Trade Union of Nigeria ne sashe na 17.
Shin ko babbar hedkwata ta kasa ta taba jawo hankalin hukumar gudanarwar jami’ar dangane da abinda ke faruwa?
Dukka kwafin wasikun dakatarwa da kuma na kora duk an mikawa hukumar gudanarwar kwafi, an ba shugaban jami’a, don haka shugaban jami’ar ya san cewa an rigaya an kore shi, to idan shugaban jami’ar ya san cewa an kore shi wannan na nuna cewa bai kamata su yarda su amince da a yi wani taron da ba kan doka ba a cikin dakunan taro.
A takaice domin amfanin masu karatu, waye daga cikinku ku biyun babar kungiyar SSANU ta kasa bangaren zartarwa ta san da matsayinsa a shugaaba a halin yanzu?
Sai kwamared ya ce, hukumar zartarwar SSANU ta kasa kawai ta san da zaman Kwamared Shu’aibu Khalil ne wanda ni ne, a matsayin ciyaman mai cikakken iko na kungiyar SSANU reshen jami’ar ABU.
Dalilan su ne duk wasu sanarwa zuwa reshen na zuwa gareni ne, kuma duk wata gayyata zuwa taron zartarwa na kasa domin a wakilci wannan reshen yana gareni ne, a yanzu da na ke yi maka magana na dawo kenan daga taro karo na 35 da ake yi a kai a kai na kungiyar SSANU ta kasa ne wanda aka yi a Enugu State Unibersity of Technology, a yanzu da nake yi maka magana. To amma a lokacin da muke yin wancan taro, Kwamared I.A Bello shi kuma yana yin wani taron karawa juna sani wanda ba kan ka’ida ya ke ba a wannan reshe yana kuma nuna cewa shi ne ciyaman, shin wannan ba abin dariya ba ne? Wani zai kira shi ciyaman bayan duka ciyamomin na Nijeriya gaba daya sun taru a dakin taro daya na gabaki daya jami’o’in Nijeriya, shin me ya sa shi ba shi? Me ya sa ba ya nan? Can ya kamata ya kasance. A lokacin ne kuma daidai wannan taron karawa juna sanin aka yi shi, kuma ba kan ka’ida bane ya karya dokar kungiya a yi taro daidai da lokacin da babban taron kasa ke gudana, wannan ya karya dokar kungiya kuma ya karya tsare-tsarenta. Dan haka duk abubuwa da ya tattauna a wajen wanna taro na karawa juna sani bashi kan doka kuma ba da wani tasiri. Yana dai kawai yaudarar kansa ne da kuma wasu ‘yan mambobi da ke sauraronsa a reshen.
To yanzu da babbar kungiyar kasa ita dai kai ne ta sani a matsayin shugaban wannan kungiya mai cikakken iko, ita kuma jami’a ta nuna ta amince shi ne, to miye zai kasance mafita wadda za a warware wannan matsalar a nan gaba?
Wannan hakki ne na babbar kungiyar SSANU ta kasa ta shigo ciki, ya kamata su shigo su jawo hankalin jami’a domin su yi abinda ya kamata. Dan saboda sashe na 25 na dokar kungiyar Trade Union ta tanadar cewa dole ne mai daukar aiki ya nuna amincewa da Trade Uniin , doka ce. To idan doka ce shugabancin jami’ar ya kamata ya amince da babbar kungiyar SSANU ta kasa, ya kamata ma dai ka sani cewa ba shi ne kace na ce na farko tsakanin kungiyoyi ba a jami’ar Ahmadu Bello, wasu shekarun da suka gabata akwai wani abu mai kama da haka a ASUU, ASUU ta dakatar da shugabancin reshen nan ABU su kuma wadanda aka dakatar din suka shugar da karar babbar kungiyar, suna kalubalantar babbar kungiyar a National Industrial Court Kano, to amma da aka daga shari’ar zuwa sati biyu zuwa wata biyu, hukumar da ke ABU suka fitar da sanarwar cewa su ba yadda za su yi sai su amince da shugabancin da babbar kungiyar ta kasa ta amince da shi , kuma abinda ya faru kenan. Hanya daya da za a warware wannan rikita-rikatar tsakanin kungiyoyi in ta afku shine hukumar ta yi hakan, domin a warware al’amarin, to amma a bangaren SSANU muna ganin wani abu ne daban, muna ganin to Kwamared Shu’aibu ka tsaya sai mun ga karshen abinda shi Kwamared I.A Bello ya shigar wanda yanzu ya ke a bayyana, shin me ya sa zai zama haka? Wannan ba shi ne misalin da zan baka ba kawai, a NASSU ma an sami kwatankwacin haka, an shigar da koken cewa shugabancin NASSU ba su kai kammalallun Chekue of dues, zuwa ga babbar kungiyar NASSU, ita kuma NASSU ta dakatar da shugabancin reshen ta nada na rikon kwarya, jami’ar Ahmadu Bello ta amince da shugabancin rikon kwaryar duk kuwa da cewa wadanda aka dakatar din sun tafi National Industrial Court sun shigar da kara suna kalubalantar dakatarwar, me ya sa ake yin wani abu daban a SSANU?
To amma ka je a hukumance ka sanar kungiyar ta kasa a kan wannan?
Tabbas, na je na sanar da su a hukumance, domin ba na so kungiyar ta kasa su yi tunanin kamar bana yin aiki na ne, a matsayina na shugaban SSANU mai cikakken iko na reshen jami’ar Ahmadu Bello. Domin idan babbar kungiyar ta ji cewa korarren shugaban yana gudanar da tarurruka, taron karawa juna, taro da ‘yan jaridu zai nuna kamar bana aiki na ne, ba tare da sun san cewa akwai wasu matsaloli ba, to dole in shaidawa babbar kungiyar kasa, domin suyi abinda ya dace su yi, ni ba zan fito in yi fito-na-fito da wani ba, ni Kwamared ne mai son zaman lafiya, to domin ni mai son zaman lafiya ne ba zan fito in fara ta hanyar fada ba cewa sai na karbisakatariya da karfin tsiya ko in tursasa hukumar gudanarwa kada su amince da Kwamared I.A Bello, jami’ar Ahmadu Bello jami’a ce da sauran jami’o’i ya kamata su zo su koyi abubuwa, to hukumar gudanarwar jami’ar ya kamata su yi abinda ya kamata, ya dace su yi abinda ya kamata. Sun yi maganin abinda ya faru a ASUU kuma sun warware shigen haka da ya faru a NASSU, ta hanyar yarda da shugabancin da manyan kungiyoyin na kasa suka amince da shi wanda ya ke a kan doka.