Tsohon dan wasan Manchester City, Danny Mills, ya bayyana cewa abune mai wahala a iya samun kungiyar da zata iya takawa Manchester City burki a gasar firimiyar bana da ake bugawa da kuma ragowar kofunan da kungiyar take fafatawa a Ingila.
Danny Mills ya bayyana hakane bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta doke Arsenal har gida a gasar firimiya sannan ta kai karawar dab da na kusa da na karshe wato Kuarter finals a gasar FA Cup bayan da ta doke Swansea 3-1 ranar Larabar satin daya gabata. Wannan nasarar ta sa Manchester City ta yi wasanni 18 a jere a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba kuma wadanda keda tarihin cin wasanni 14 a jere a Ingila sun hada da Preston a kakar wasa ta 1891 zuwa 1992 da bajintar da Arsenal ta yi a shekarar 1987 zuwa 1988.
Har ila yau Manchester City ta kai wasan karshe a Caraboa a bana, inda za ta fafata da kungiyar kwallon kafar Tottenham wadda Mourinho yake koyarwa cikin watan Afirilu kungiyar ta Etihad tana jan ragamar teburin Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da Manchester United ta biyu.
Haka kuma Manchester City tana buga gasar Champions League, inda za ta buga fafatawar zagaye na biyu a wasan farko da Borussia Monchengladbach saboda haka kungiyar na sa ran lashe Caraboa na bana da fa Cup da Premier League da kuma Champions League.