Wayoyin Balackberry Na Gab Da Shiga Kwandon Tarihi

Tare da Baƙir Muhammad

A shekarun baya wayoyi ƙirar blackberry su ne wayoyin alfarma na ƙece raini, takamar duk wani ɗan ƙwalisa shine ya samu wayar Blackberry ya dinga shanawa da ita, a cikin ƙawaye da abokai mai amfani da wayar Blackberry tamkar sarki ake kallon sa, saboda lokacin da wayoyin Blackberry su ka fara fita duk wayoyin da suke hannayen jama’a ba su da wasu abubuwa na sha’awa, misali daukar hoto ko kallon bidiyo, sannan ba su da daɗin shiga intanet (browsing), wayoyin dukn akasarin su tsarin Jaɓa suke amfani da shi sai ƙalilan ma su amfani da tsarin Symbian.

Fitowar wayoyin Blackberry ya matuƙar kawo sauyi a kasuwar wayoyi, ta inda duk wayar da Blackberry ba ce to ba’a ma ta wani kallon arziki, kuma tabbas hakan ne in ka dauki abubuwan da wayoyin Blackberry suke kunshe da su za ka ga lalla duk wayar da ba Blackberry ba to tamkar bambamcin birnin da ƙauye ne, ba bau ma mai tunanin watan watarana wayoyin za su daina tashe har ma a manta da su.

Fitowar wayoyin Android da iPhone shi ne babban abinda yayi wa kasuwar wayoyin Blackberry cikas, saboda waɗannan wayoyin sunzo da tsarin da ya yi ma na Blackberry fintinkau nesa ba kusa ba, kuma suna da saukin aiki tsaɓanin wayoyin Blackberry, duk da su ma suna da tsada amma wannan bai hana ma su amfani da wayoyi watsar da wayoyin Blackberry ba, wannan ya sa kasuwar wayoyin na Blackberry ta matuƙar ɗurƙushewa.

A yanzu babu wata waya ta Blackberry da ta isa ta haɗa kanta da wayoyin da ake yayi na Android da iPhone ku kusa, duk da ba’a daina ƙera wayoyin Blackberry ba, amma labarinsu ya fara shiga kwandon tarihi, duk suna yin wasu yan dabaru da suke ganin hakan zai iya dawo da martabar wayar ta su a kasuwannin wayoyi, haka na da kamar wuya.

An ƙiyasta a shekara a na siyan wayoyin Android aƙalla miliyan 296.9 wayoyin iPhone kuwa ana siyan miliyan 44.4, su kuma wayoyin Blackberry 400,000 kacal ake siya, duk ba lallai bane wayoyin su shiga kwandon tarihi amma bisa ga dukkan alamu hakan ba makawa sai ya faru.

Wayoyin Android sune suka cika kasuwar wayoyi a duniya inda suka wuce duk wayoyin da ba su a kasuwa, watakila sauƙin kuɗi, sauƙin samuwa, sauƙin amfani da kuma yayi ya sa wayoyin Android suka yi ma sauran wayoyi fintinkau a kasuwanni, wasu masu hasashe ma suna ganin nan da yan shekaru za a daina amfani da wasu wayoyi sai Android kaɗai, wasu kuma suke ganin wani sabon tsarin manhajjar waya zai fito da zai yi gasa da da Android, lokaci ne kaɗai zai fayyace mana wannan.

Akwai wasu tsarin wayoyin ma, wato Microsoft window wanda kamfanin Nokia suke ƙerawa, su ma suna fuskantar barazana irinta Blackberry ɗin, duk da kamar sun fi wayoyin Blackberry tasiri a yanzu, amma su ma dai makomar su ɗaya ne, saboda basu da tsari da ya dace da buƙatun masu amfani da wayoyin hannu a yanzu, kamfanonin waɗannan wayoyin suna ta ‘yan dabaru da zai magance wannan matsalar, amma kamar dabarun nasu baza su yi amfani ba, na gaba ya yi gaba…….

Exit mobile version