Idris Aliyu Daudawa" />

WHO Da UNICEF Sun Bayyana Amfanin Shayar Da Jariri Nonon Uwa

Hukumar lafiya ta duniya ko kuma WHO da kuma asusun kula da al’amuran gaggawa na kananan yara UNICEF, sune suka yi kira da gwamnatocin duniya da su cigaba da wayar da kan mutane akan amfanin shayar da jarirai nonon Uwa har na tsawon akalla watanni shida bayan haihuwarsu.

Kungiyoyin sun yi shi wannan kiran ne a shafinsu na yanar gizo a makon su na wayar da kan mutane mahimmancin shayar da jarirai nono a ranar shayarwa ta duniya wadda ake yi daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Agusta na ko wacce shekara.

A jawaban da suka yi shugabanin UNICEF ko kuma Hukumar kula da al’amuran gaggawa na kananan yara Henrietta Fore da na ita Hukumar lafiya ta duniya, WHO Tedros Ghebreyesus sun bayyana cewa, shayar da jariri nonon Uwa yana da mahimmanci saboda nono yana kunshe da sinadarin dake inganta kiwon lafiyar yaro musamman ma na kariya daga kamuwa da cututtukan da suke kashe kananan yara.

Shugabanin sun kara da cewa yin haka zai taimaka wajen ceto rayukan yara 820,000 da suke mutuwa duk shekara a duniya.

Mahimmancin shayar da jariri nonon Uwa:

Likitoci sun bayyana shayar da jariri nono kadai musamman na tsawon watanni shida ko kuma fiye da haka abu ne wanda yake kara da kuma kare lafiyar jarirai.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa kasa da kashi 24 cikin 100 na jarirai ne suke samun damar shayarwar manufa anan ita ce shan nono Uwa na tsawon watanni shida a Nijeriya.

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Chimay Thompson ya bayyana haka, bugu da kari kuma ya kara da cewa rashin yin haka na daya daga cikin dalilin dake kara yawan mace-macen yara da mata.

 

Exit mobile version