Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ta ce za ta tura zubi 11,000 na alluran rigakafin cutar Ebola, da kuma kwararru sama da 100 zuwa Guinea, don shawo kan barkewar cutar Ebola a wannan kasa ta Afirka ta Yamma.
Da ta ke jawabi ta kafar bidiyo a babban taron manema labarai daga hedikwatarta da ke Brazzabille, Janhuriyar Congo, Daraktar hukumar ta WHO shiyyar Afurka, Matshidiso Moeti, ta ce jami’ai na kuma sa ran samun karin zubi 8,600 na alluran rigakafi daga Amurka, wanda zai sa jimlar alluran rigakafin ya kai 20,000.
Haka kuma hukumar na sa ran isar alluran zuwa ranar Lahadi, sannan kuma za a fara rigakafin Ebolar zuwa ranar Litini.
Jami’an lafiya a kasar ta Guinea, sun ayyana tsananin cutar yanzu a matsayin annoba a ranar Lahadi, bayan da aka kara samun karin mutane biyu da su ka kamu da cutar a Gouecke, wani kauye a lardin N’Zerekore.